In Kura Tana Maganin Zawo Tai Wa Kanta Mana martanin Keyamo Ga Atiku Kan Kwangila

In Kura Tana Maganin Zawo Tai Wa Kanta Mana martanin Keyamo Ga Atiku Kan Kwangila

  • Kasa da kwana talatin da bakwai ya rage ya kada kuri'u a akwatin nan zabe a Nigeria dan zabar sabbin shuwagabbanin
  • Aman muryoyin juna ya yi yawa wajen suka ko yabon dan takara daga magoya baya da kuma hadimansu
  • Fetus Keyamo da yake a matsayin mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa shima yayi wata magana game da Atiku

Abuja - Festus Keyamo mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben jam'iyyar APC, ya magantu kan wani maganar da aka jinginawa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, rahoton The Cable.

Yayin da yake magana a ranar Larabar nan, a wani taron masu ruwa da tsaki da aka shirya a Abeokuta, Atiku yayi alkawarin bayar da kwangila ga wadanda suka tabbatar PDP ta lashe mazabarsu.

Kara karanta wannan

2023: Mutane Za Su Yi Alfahari da Kasancewarsu Yan Najeriya Idan Na Gaje Buhari, Peter Obi

"Idan kuka zabe ni shugaban kasa, kuma kuka zo kuka ce kuna son a baku aiki ko kwangila, zan tambayeku ina sakamakon mazabarku, shi ka kawota ko kuwa, a haka ne kawai zamu tabbatar da wanda sukai mana bauta har mu ka ci zabe" inji Atiku.
Atiku
In Kura Tana Maganin Zawo Tai Wa Kanta Mana martanin Keyamo Ga Atiku Kan Kwangila Hoto: UCG
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Bai kamata ku ringa bin gwamnoninku da yan majalissar ku, alhalin kana da aiki a mazabarka ba, dole ka kawo mazabarka in kana son ka samu kwangila ko kuma aiki, sai ka tsaya ka tabbatar da nasarar jam'iya a akwatinka"

Martanin Keyamo kan batun Atiku

Yayin da yake maida martani a shafinsa na Twitter, mai magana da yawun kwamitin yaki neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, Festus Keyamo yace:

"Atiku ya manta cewa al'umma ake bawa kwangila ba wai yan jam'iyyya ba"

Kara karanta wannan

Ba Wanda Zai Ci Bulus: Atiku Ya Gindaya Sharadin Baiwa Mambobi da Manyan PDP Mukami Idan Ya Ci Zabe

"Ai ba'a canjawa tuwo suna"
"Ya manta cewa kwangila al'umma ake bawa, kuma doka ce tace ai hakan, Sarkin azarbabi!"

Ga abinda Festus din ya wallafa a shafin nasa:

Hukumar zaben Nigeria

Hukumar zaben Nigeria tace zuwa yanzu akwai yan Nigeria kimanin mutum miliyan tamanin da doriya da sukai rijistar zabe.

Hukumar tace akwai akwatunan jefa kuri'a guda 176,846 da ke fadin kasar nan baya da jam'iyyu 18 da zasu fafafa a zaben watan gobe da yake karatowa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel