Ya'yan APC Biyu Sun Kwanta Dama Sanadin Hatsarin da Ya Rutsa da Su a Ebonyi

Ya'yan APC Biyu Sun Kwanta Dama Sanadin Hatsarin da Ya Rutsa da Su a Ebonyi

  • Wani mummunan hatsarin ya rutsa da motar da ta ɗauko mambobin jam'iyar APC a jihar Ebonyi ranar Laraba
  • Wani ganau ya bayyana cewa lamarin ya faru ne sakamakon rashin kular Direbobi kuma mutane biyu sun mutu nan take
  • An tattaro cewa magoya bayan APC na hanyar zuwa wurin kaddamar da kamfen dan takarar gwamna a karamar hukumar Izzi

Ebonyi - Akalla mambobin jam'iyyar APC biyu ake fargabar sun rasu sakamakon wani mummunan hatsari da ya rutsa da su ranar Laraba a jihar Ebonyi.

Jaridar Punch ta tattaro cewa hatsarin ya faru ne a kan Titin Onuebonyi daidai mahaɗar Sharon da ke karamar hukumar Izzi, jihar Ebonyi a kudu maso gabashin Najeriya.

Taswirar jihar Ebonyi.
Ya'yan APC Biyu Sun Kwanta Dama Sanadin Hatsarin da Ya Rutsa da Su a Ebonyi Hoto: punchng
Asali: Twitter

Bayanai sun nuna cewa mambobin jam'iyya man mulkin na cikin Motar da suka ɗauko shata mallakin kamfanin Sufurin Motocin Onitsha ta Kudu.

Kara karanta wannan

An Kama Sarakuna Biyu da Hannu a Garkuwa da Fasinjojin Jirgin Kasa a Najeriya

Hadarin ya rutsa da su a hanyar zuwa Iboko, hedkwatar karamar hukumar Izzi, wurin da aka shirya kaddamar da kamfen ɗan takarar gwamnan jihar na APC, Francis Nwifuru, wanda ya gudana ranar Laraba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bincike ya tabbatar da cewa mutanen biyu sun mutu ne nan take sanadin hatsarin kuma an ce waɗan da suka rasu namiji ne da mace saura kuma sun ji raunuka.

Wani ganau da ya nemi a sakaya bayanansa ya yi bayanin cewa hatsarin ya faru ne saboda rashin kula da ka'idoji na Direbobi, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Ya ce:

"Ɗaya daga cikin Direbobin yana tafiya babu kula bisa rashin sa'a ya yi taho mu gama da wata Mota a kokarin wuce wa wata ba tare da damuwa da rayuwarsa da ta Fasinjoji ba."
"Na ga an ɗauki wadanda hatsarin ya shafa zuwa Asibiti amma ina da tabbacin mutum biyu a ciki, namiji da mace sun mutu nan take, abun ba dadin gani."

Kara karanta wannan

Babbar Nasara: Luguden Bama-Bamai Ya Sheke Daruruwan Yan Bindiga a Jihar Arewa 1

Duk wani yunkuri na jin ta bakin hukumar kiyaye haɗurra rashen jihar Ebonyi bai kai ga nasara ba. An ce hukumar ta tura sabon kwamanda kuma ba zai iya cewa komai ba a halin yanzu.

APC ta rasa mambobi a jihar Katsina

A wani labarin kuma Ana Gan da Zabe, Bola Tinubu Ya Gamu da Babbar Matsala a Jihar Shugaba Buhari

Yayin da ya rage kwanaki kasa 40 zaben shugaban kasa, jam'iyyar APC da Bola Tinubu ke takara ta rasa dubannin mambobi a jihar Katsina.

Lamarin ya faru ne yayin da tawagar yakin neman zaben Atiku/Lado na PDP ya kai ziyarar kamfe karamar hukumar Iingawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel