Abubuwa Masu Fashewa Sun Tashi a Wurin Kamfen din APC a Fatakwal

Abubuwa Masu Fashewa Sun Tashi a Wurin Kamfen din APC a Fatakwal

  • Bama-bamai biyu sun tashi ana tsaka da zagayen kamfen na jam'iyyar APC a filin wasan Rumuwoji cikin Port Harcourt babban birnin jihar Ribas
  • Kamar yadda rahoto ya bayyana, lamarin ya ritsa da mutane uku, biyu mata daya namiji, inda aka garzaya da su asibiti don ceto rayuwarsu
  • Sakataren watsa labarai na APC, Darlington Nwauju ne ya tabbatar da aukuwar lamarin, wanda ya siffanta a matsayin abun takaici

Fatakwal, Ribas - A kalla mutane uku sun samu raunuka ranar Alhamis, yayin da wasu abubuwa masu fashewa suka tashi a zagayen kamfen din APC a filin wasan Rumuwoji cikin Port Harcourt, babban birnin jihar Ribas.

Ralin APC a Fatakwal
Abubuwa Masu Fashewa Sun Tashi a Wurin Kamfen din APC a Fatakwal. Hoto daga punchng.com
Asali: UGC

Biyu daga cikin wadanda suka samu raunukan mata ne, inda duk aka garzaya da su asibiti don ceto rayuwarsu.

Sakataren watsa labarai na APC, Darlington Nwauju ne ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya siffanta hakan a "abun alhini,".

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Atiku Abubakar Ya Dira Jihar Matashin Gwamnan G-5, Ya Shiga Matsala Tun a Filin Jirgi

Sai dai kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Iringe-Koko ya ce zai bawa wakilin Punch cikakken bayanin kan lamarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Karin bayani na tafe...

Asali: Legit.ng

Online view pixel