Kyau Kwankwaso Ya Hakura – Kungiya ta Kawo Hujjoji Kan Wanda Arewa Za Ta Zaba

Kyau Kwankwaso Ya Hakura – Kungiya ta Kawo Hujjoji Kan Wanda Arewa Za Ta Zaba

  • Wata kungiya ta masu neman ceto ‘Yan Arewa ta aika da sako na musamman zuwa ga Rabiu Musa Kwankwaso
  • Kungiyar Northern Liberal Democratic Movement ta na so ‘dan takaran NNPP ya janyewa Atiku Abubakar a 2023
  • Sakataren NLDM yana ganin za iyi wahala Rabiu Kwankwaso ya kai labari, don haka zai fi kyau ya bi bayan PDP

Abuja - Wata kungiya mai suna Northern Liberal Democratic Movement, wanda aka kafa dominn ceto al’umma, ta sa baki a kan harkar zaben 2023.

Vanguard ta kawo rahoto a yammacin Juma’a cewa kungiyar NLDM ta na so Rabiu Musa Kwankwaso ya hakura da neman shugabancin Najeriya.

Kungiyar ta na so ‘dan takaran na jam’iyyar NNPP ya janyewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar mai rike da tutar PDP a bana.

Kara karanta wannan

‘Dan Takarar M/Gwamna Ya Juyawa Jam’iyyarsa Baya, Za a ba Shi Kujera a Mulkin APC

A cewar wannan kungiya ta mutanen Arewa, jama’a da masu ruwa da tsakin yankin sun fi karkata ne a kan ‘dan takarar jam’iyyar PDP a kan na NNPP.

Sakataren NLDM ya yi jawabi

Babban Sakataren NLDM na kasa, Hon. Balarabe Ali Bello ya fitarwa manema labarai da wannan jawabi a garin Abuja a ranar 18 ga watan Junairu 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hon. Balarabe Ali Bello yana ganin a yadda siyasar Najeriya take juyawa, zai fi yi wa Atiku Abubakar saukin lashe zabe a kan tsohon Gwamnan Kano.

Kwankwaso
Taron Kwankwaso da NNPP a Nasarawa Hoto: @SaifullahiHon
Asali: Twitter

Ana sauya-sheka daga NNPP

Daily Trust ta ce Sakataren kungiyar ya kara da cewa a yankin Arewa, jiga-jigan jam’iyyar NNPP sun sauya-sheka zuwa PDP saboda Atiku Abubakar.

A ‘yan kwanakin bayan nan, jam’iyyar adawa ta NNPP mai kayan marmari ta rasa ‘dan takarar kujerar mataimakin Gwamna a jihohin Neja da Yobe.

Kara karanta wannan

Kwankwaso Ya Yi Maganar Janye Takara, Ya Fadi Abin da Zai Sa Ya Hakura da Neman Mulki

Baya ga haka shugaban jam’iyyar na reshen Kaduna da sakatarenta a Arewa maso gabas sun canza sheka, wannan ya sa NLDM ta fi ganin nasarar PDP.

Lura da wadannan dalilai, Balarabe Ali Bello ya yi kira ga Rabiu Musa Kwankwaso a madadin ‘yan kungiyar NLDM da cewa ya janye takarar da yake yi.

"Kamar sauran mutanen Arewa, ina kira ga Mai girma Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya sake tunani domin kishin mutanenmu.
Ya kyale Wazirin Adamawa ya lashe zabe mai zuwa. Akwai sauran shekaru a gaban shi, zai iya samun wasu damammakin nan gaba."

- Hon. Balarabe Ali Bello

Dr. Babayo Liman ya bi Atiku Abubakar

Kun samu rahoto a baya cewa wanda Rabiu Musa Kwankwaso ya dogara da shi a Arewa maso gabas, Dr. Babayo Limanm ya fice daga jam’iyyar NNPP.

Dr. Babayo Liman ya ajiye mukamin Sakataren NNPP a yankinsa da jagorancin Kwankwasiyya, ya yi kira ga mabiyansa su zabi Atiku Abubakar a 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel