PDP Ta Yi Gagarumin Kamu Gabannin Zaben 2023, Babban Mai Daukar Nauyin APC a Delta Ya Koma Jam'iyyar

PDP Ta Yi Gagarumin Kamu Gabannin Zaben 2023, Babban Mai Daukar Nauyin APC a Delta Ya Koma Jam'iyyar

  • Yan kwanaki kafin babban zaben shugaban kasa na 2023, jam'iyyar PDP ta yi babban kamu a Delta
  • Babban mai daukar nauyin APC da mabiyansa sama da 3000 sun fice daga jam'iyyar a jihar ta kudu
  • Cif Tony Amechi ya ce ya gano cewar jam'iyyar mai mulki a kasar bata nufin mutane da alkhairi don hala ya raba jaha da ita

Delta - Wani babban mai daukar nauyin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a yankin Ndokwa da ke jihar Delta, Cif Tony Amechi, ya sauya sheka zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) tare da dubban mabiyansa.

Amechi ya yi bayanin cewa jam’iyyar bata taba nufin mutane da alkhairi ba don haka ba zai ci gaba da hulda ko daukar nauyin jam’iyyar da ba za ta amfani al’umma ba, rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

Ana Saura ‘Yan Kwanaki Zabe, Rikicin Cikin Gida Yana Wargaza Jam’iyyar APC

PDP da APC
PDP Ta Yi Gagarumin Kamu Gabannin Zaben 2023, Babban Mai Daukar Nauyin APC a Delta Ya Koma Jam'iyyar Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Ya kuma bayyana cewa jam’iyyar mai mulki a kasar cike take da mutane masu halayya da ke bukatar tambaya.

Taron sauya shekar wanda ya gudana a garin Aboh, karamar hukumar Ndokwa ta gabas ya samu halartan shugaban PDP reshen jihar Delta, Barista Kingsley Esiso, Injiniya Dan Ossai da dan takarar mataimakin gwamna, Cif Monday Onyeme da sauran jiga-jigan jam’iyyar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Amechi ya ce:

“Ina yiwa Ndokwa yaki a matsayin dan kasa mai zaman kansa amma aka yaudare ni zuwa APC, bayan dan lokaci na gano cewa babu haske a APC.
“Na dauki tsawon lokaci ina nazarin dukkanin yan takara a Ndokwa kuma na ga cancanta tattare da Onyeme, mutum mai zuciyar alkhairi kuma yana nufin mutane da alkhairi. Wannan ne dalilin da yasa tikitin Sheriff da Onyeme ya zama kamar anyi an gama, kuma saboda wannan dalili dole mu yi wa PDP aiki a zabe mai zuwa. Shugabanci ba iya girma bane illa yin abun da ya dace.”

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Daya Daga Cikin Gwamnonin G-5 Ya Sauya Tunani, Zai Hade da Atiku Abubakar

Ni da mabiyana 3000 mun hade da PDP a Ndokwa, Amechi

Ya ci gaba da cewa:

“Na ayyana komawata PDP tare da mabiyana sama da 3000. Za mu rushe APC a kasar Ndokwa gaba daya saboda basu taba nufinku da alkhairi ba. Dukkaninsu sun kasance a PDP amma kawai sai suka sauya wani riga don yaudararmu. Hawainiya ba zai taba sauya wurinsa ba."

Esiso wanda ya tarbi masu sauya shekar ya yaba ma Amechi kan wannan mataki da ya dauka yana mai cewa zuwansa tare da magoya bayansa zai kara daraja ga jam’iyyar.

Mujallar Oasis ta nakalto Esiso yana cewa:

“Abun da ke faruwa a nan a yau ya nuna cewa APC ta rushe a Ndokwa. Ya kamata shugabannin su gane cewa akwai karfi a hadin kai. Idan wani ya yi maka laifi a PDP dan Allah ka yi hakuri ka yafe. Babu amfanin gaba. Babu wanda zai iya shi kadai.

Kara karanta wannan

2023: Sabon Matsala Ga Kwankwaso Yayin Da Yan NNPP 700,000 Suka Koma PDP a Jihar Arewa, Sun Bada Dalili

“Mun kasance a nan don yiwa dan uwanmu Cif Amechi wanda ya dingi yawo a APC Da tsintsiya kamar maye maraba. Muna maka barka da zuwa jam’iyyar lema. Muna matukar farin ciki da zuwanka kuma muna so ka sani cewa za ka ci amfanin da tsoffin mambobin jam’iyyar ke ci."

Zan mayar da Najeriya kasar da kowa zai yi alfahari da ita idan na gaji Buhari, Obi

A wani labari na daban, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar LP, Peter Obi, ya ce zai bunkasa harkar noma sannan ya kare rayuka da dukiyoyin yan Najeriya idan ya lashe zabe a 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel