2023: Dan Takarar Mataimakin Gwamna Ya Sauya Sheka Zuwa APC

2023: Dan Takarar Mataimakin Gwamna Ya Sauya Sheka Zuwa APC

  • Dan takarar mataimakin gwamna na SDP kuma shugaban matasan Kuros Riba ya sauya sheka zuwa APC mai mulki
  • Daniel Obo, shugaban kungiyar matasa NYCN yace ya koma APC ne saboda ganin nan ne inuwar matasa
  • Ya yi kira ga matasan Kuros Ribas su tabbata sun mallaki katin zabe domin kare kimarsu da gobensu

Cross River - Ɗan takarar mataimakin gwamna a jihar Kuros Riba karkashin inuwar jam'iyyar SDP, Daniel Obo, ya sauya sheka zuwa All Progressives Congress (APC), kamar yadda Premium times ta ruwaito.

Ɗan siyasan ya samu tarba mai kyau daga shugaban APC na gundumar Obubra Urban, Daniel Okpa, bayan ya yi rijista kuma ya karbi katin zama cikakken ɗan jam'iyya.

APC a Kuros Riba.
2023: Dan Takarar Mataimakin Gwamna Ya Sauya Sheka Zuwa APC Hoto: premiumtimesng
Asali: UGC

Da yake jawabi, Mista Ubo, shugaban kungiyar matasa (NYCN) reshen Kuros Riba yace ya dauki matakin komawa jam'iyyar APC ne saboda ita ce ta matasa.

Kara karanta wannan

Atiku, Tinubu Ko Obi? An Faɗi Wanda Tuni Aka Cire Shi Daga Tseren Zama Shugaban Kasa a 2023

A cewarsa, gwamna Ben Ayade na jihar Kuros Riba, "Ya matso da jagoranci da gwamnati kusa za al'umma ta hanyar naɗa matasa sama da kaso 80 a majalisar gwamnatinsa."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Haka nan yace ya zaɓi shiga APC ne domin ya taimaka wa yan takarar jam'iyyar su yi nasara a zabe. A kalamansa ya ce:

"Ni wakilin matasa ne kuma a shirye muke mu tsayawa matasa a jiharmu. APC a Kuros Riba ta agazawa matasa kuma ta basu tikitin takara. Mun fahimci cewa karfin mu na tare da APC."
"Wannan dalilin ne yasa muka shiga jam'iyyar don kare matasa. A yau muna da shugabannin matasa a matakin kananan hukumomi 18 waɗanda suka biyo ni zuwa APC."
"Haka nan shugabannin SDP na gundumomi sama da Tara ne suka biyo ni zuwa APC. Akwai daruruwan matasan da suka take mun baya domin kare kimarsu a zamaninsu."

Kara karanta wannan

Babban Mai Daukar Nauyin APC da Dubban Mabiyansa Sun Bar Tafiyar Tinubu, Sun Koma PDP

Bayan nan matashin ɗan siyasan ya yi kira ga matasan Kuros Riba su garazaya su mallaki katin zabe kuma su fito kwansu da kwarkwata su zabi 'yan takarar APC.

Dubbannin Mambobin APC Sun Koma PDP a Jihar Shugaba Buhari

A wani labarin kuma Dubbannin mambobin (APC) sun sauya tunani sun koma jam'iyyar PDP a karamar hukumar Ingawa ta jihar Katsina.

Shugaban PDP reshen jihar Katsina, Lawal Magaji Danbaci, shi ne ya bayyana haka wurin Ralin wanda ya samu halartar dubun dubatar magoya bayan PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel