Bayan Tafiyar Atiku, Obasanjo Ya Nuna Boyayyar Hikimar Goyon Bayan Peter Obi

Bayan Tafiyar Atiku, Obasanjo Ya Nuna Boyayyar Hikimar Goyon Bayan Peter Obi

  • Olusegun Obasanjo ya kare kan shi daga masu sukarsa saboda yana goyon bayan Peter Obi a 2023
  • Tsohon shugaban na Najeriya ya ce kasar nan ba ta bukatar shugaban da bai da halin kwarai
  • Obasanjo ya ce Ubangiji zai tambaye shi idan har ya boye gaskiyar da ya sani a kan masu takara

Ogun - Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo ya yi bayanin abin da ya sa ya fito, ya shaidawa al’umma yana goyon bayan Peter Obi a zaben bana.

Da yake jawabi a ranar Alhamis, 19 ga watan Junairu 2023, Daily Trust ta rahoto Olusegun Obasanjo yana cewa ba a bukatar shugaba mai halin banza.

Obasanjo ya yi wannan bayani ne a wajen wani zama da TEL-Africa ta shirya domin a tattauna abin da ya shafi shugabancin al’umma a kasashen Afrika.

Kara karanta wannan

Shekaru 30 da Rushe Zabe, Obasanjo Ya Tona Abin da Ya Hana a Mikawa Abiola Mulki

Jaridar ta ce taken zaman da aka yi da Obasanjo a matsayinsa na jagora, shi ne “Executive Decisions, Indecisions, & Leadership Development in Africa.”

Obasanjo ya yi wa Obi mubaya'a?

Cif Obasanjo bai zargi sauran ‘yan takaran kujerar shugaban kasar da halayen banza ba, amma ya nuna tsohon gwamnan Anambra ya fi morar hali nagari.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon shugaban kasar yake cewa a wasikar da ya fitar, bai ce ya yi wa Obi mubaya’a ba, illa iyaka ya fadi ra’ayinsa ne kurum a kan sauran ‘yan takaran.

Obasanjo
Olusegun Obasanjo Hoto: Getty Images
Asali: UGC

A cewar Obasanjo, tun da ya rubuta wannan wasika, ya san za ayi ta sukarsa, yake cewa Ubangiji zai tambaye shi idan bai sanar da mutane gaskiya ba.

Cif Obasanjo mai shekaru 85 ya ce ya gagara gane mutane domin a baya ya fadi gaskiya a kan Muhammadu Buhari, kuma hakan bai nufin ya bata shi.

Kara karanta wannan

Kwankwaso Ya Yi Maganar Janye Takara, Ya Fadi Abin da Zai Sa Ya Hakura da Neman Mulki

Atiku ya je kamfe a Ogun

Wannan magana da tsohon shugaban Najeriyan ya yi ta zo daidai da ranar da Atiku Abubakar ya ziyarci Ogun domin yakin neman zabensa a jam’iyyar PDP.

Legit.ng Hausa ta fahimci ‘dan takaran bai kai wa tsohon mai gidansa ziyara ba wannan karo.

Wasikar Obasanjo ta sabuwar shekara

A wasikar da ya rubutawa mutanen Najeriya na taya su murnar shiga sabuwar shekara, an ji labari Obasanjo ya nuna cewa yana goyon bayan LP ne.

Goyon bayan da Obasanjo ya ba ‘dan takaran na jam’iyyar LP ya jawo surutu daga bangaren Bola Tinubu, Atiku Abubakar da Rabiu Musa Kwankwaso.

A dalilin haka ne aka bijirowa tsohon sojan da wannan magana a wajen wannan taro da aka yi dazu, shi kuma ya kare kan shi a kan matsayar da ya dauka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel