2023: Sabon Matsala Ga Kwankwaso Yayin Da Yan NNPP 700,000 Suka Koma PDP a Jihar Arewa, Sun Bada Dalili

2023: Sabon Matsala Ga Kwankwaso Yayin Da Yan NNPP 700,000 Suka Koma PDP a Jihar Arewa, Sun Bada Dalili

  • Takarar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na jam'iyyar NNPP ta gamu da babban barazana bayan sauya sheka da mutane da dama suka yi
  • Hakan na zuwa ne yayin da mambobin jam'iyyar NNPP a kalla 700,000 suka shiga jam'iyyar PDP a jihar Bauchi
  • Bugu da kari, wadanda suka sauya shekan sun yi kira ga Kwankwaso ya bi sahunsu ya hada karfi da karfe da Atiku

Bauchi - Wani rahoto da jaridar Leadership ta wallafa ya ce kimanin mutane 700,000 yan jam'iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, a Bauchi sun sauya sheka zuwa jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP.

Kuma kimanin mambobin jam'iyyar NNPP miliyan 2.8 ne a jihar ta arewa maso gabas suka fice daga jam'iyyar suka koma PDP, a cewar sakataren yanki na NNPP, Dr Babayo Liman.

Kara karanta wannan

Kayan marmari ya rube: Mambobin NNPP miliyan 2.8 sun koma PDP, sun ba Kwankwaso shawara

Bauchi
2023: Sabon Matsala Ga Kwankwaso Yayin Da Yan NNPP 700,000 Suka Koma PDP a Jihar Arewa, Sun Bada Dalili. Hoto: @TheNationNews
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wadanda suka sauya shekan sun bada dalilinsu

Liman ya bayyana hakan ne yayin taron manema labarai a Bauchi, ya ce mutane miliyan 2.8 suna wakiltar mambobi miliyan 3.5 da suka yi rajista a jam'iyyar cikin shekaru takwas da suka wuce karkashin jagorancinsa a matsayin sakataren yanki na jam'iyya.

Ya ce:

"Na yi murabus daga mukami na na sakataren jam'iyyar NNPP na yankin arewa maso gabas, kuma a matsayin mamba na kwamitin kamfen din shugaban kasa, a matsayi na na mamba na NNPP, kuma a matsayin shugaban Kwankwasiyya na Bauchi da kuma a yankin arewa maso gabas na kasar nan."

Liman ya tunatar cewa ya yi murabus a hukumance a ranar 14 ga watan Janairun 2023 amma ya sanar da murabus dinsa a fili tare da komawa PDP a jiya.

Mambobi da dama da magoya baya a yankin sun bi shi.

Kara karanta wannan

Tsohon Shugaban PDP, Dan Majalisa da Wasu Kusoshi Sun Bar Tafiyar Atiku, Sun Koma Kwankwaso

Wadanda suka sauya shekan sun aika sako ga Kwankwaso

Ya yi kira ga dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP Sanata Rabius Musa Kwankwaso ya hada karfi da karfe tare da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, don ya yi nasarar zama shugaban kasa a zaben na watan Fabrairu.

Zaben 2023: Yan takarar majalisa na NNPP sun koma jam'iyyar APC

A wani rahoton, Ibrahim Shinkafi, dan takarar sanata na Zamfara ta arewa da dan takarar majalisar wakilai na mazabar Shinkafi/Zurmi, Suleiman Garba, sun koma APC.

Tsohon gwamnan jihar Zamfara, AbdulAziz Yari ne ya tarbi Shinkafi da Garba cikin jam'iyyar na APC a ranar Talata, The Cable ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel