Jigo a Kwamitin Neman Zabe Ya Yi Maganar ‘Rigimar’ Tinubu da Gwamnonin APC

Jigo a Kwamitin Neman Zabe Ya Yi Maganar ‘Rigimar’ Tinubu da Gwamnonin APC

  • James Faleke ya ce babu rikicin da ya kaure tsakanin Asiwaju Bola Tinubu da Gwamnonin Jihohin APC
  • Sakataren kwamitin PCC ya yi bayanin abin da ya sa Bola Tinubu ya zauna da masu neman takara a APC
  • Duk da ana fama da ‘yan matsaloli, Hon. Faleke ya ce babu rashin jituwa da Gwamnoni a kan Tinubu

Abuja - Jam’iyyar APC ta ce babu komai tsakanin Asiwaju Bola Tinubu mai neman shugabancin kasa da Gwamnonin da ke mulki a APC sai alheri.

Vanguard ta rahoto Hon. James Faleke yana cewa akasin jita-jitar da ake yadawa, dangantakar Asiwaju Bola Tinubu da Gwamnoni ba tayi tsami ba.

James Faleke wanda shi ne Sakataren kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa a APC ya yi wannan bayani ne da ya zanta da manema labarai.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Fadi Wadanda Zai ba Mukamai da Abin da Zai Yi Kafin Kwana 100 a Aso Rock

Bayan ‘dan takaran ya yi zama da Gwamnonin jihohi da masu neman takaran ‘yan majalisa na APC, Faleke ya zanta da ‘yan jarida a garin Abuja.

PCC, NWC sun je taro a Abuja

Sauran wadanda suka hadu da Tinubu sun hada da shugabannin jam’iyyar APC na kasa watau NWC da kuma ‘yan kwamitin yakin neman zabensa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

NAN ta rahoto cewa shugaban APC na kasa da Ahmad Lawan sun halarci zaman da aka yi.

Tinubu da Gwamnonin APC
Neman Zaben APC Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

A cewar James Faleke, daga haduwan da aka yi a ranar Asabar, zai iya tabbatarwa mutanen Najeriya cewa APC za ta lashe zabukan da za a shirya.

Matsayar da APC ta dauka

Jaridar tace ‘dan majalisar wakilan tarayyan ya nuna makasudin zama da ‘yan takaran shi ne fahimtar halin da jam’iyyar APC take a inda suka fito.

Kara karanta wannan

Takarar 2023: Yadda Tinubu, Atiku, Kwankwaso da Obi Za Suyi Yaki a Kan Kuri’un Kano

Baya ga haka, Sakataren na PCC ya ce jam’iyyar APC za ta goyi bayan duk ‘dan takaran da INEC ta fitar da sunansa, ko da kuwa ana shari’a a kotu,

A halin yanzu Tinubu yana da kyakkyawar alaka tsakaninsa da Gwamnonin jam’iyya a jihohi.

"Ka da wanda ya saurari wadannan karyayyaki. Idan har da gaske ne, su fada. Su ne suke da matsaloli irinsu G5, G2, G1.”
A game da kalubalen da aka gabatar mana da suke fuskanta a jihohinsu, matsalar cikin gida ne da za mu shawo kan su."

- Hon. James Faleke

Ina tare da Atiku - Bala

A makon jiya aka ji labari Gwamnan Jihar Bauchi ya sanar da Mai dakin ‘dan takaran PDP, Haj. Titi Abubakar cewa yana goyon bayan mai gidanta.

Sanata Bala Mohammed yake cewa karyar banza ce mutane suke yi, su na cewa bai tare da Atiku Abubakar, ya ce yana goyon bayan ‘dan takaran na PDP.

Kara karanta wannan

Jagororin APC Sun Gaza Nunawa Tinubu Kara, Sun Kunyata Shi Wajen Yakin Zabe

Asali: Legit.ng

Online view pixel