Rikicin PDP: Gwamna Ya Gyara Zance, Ya ce Babu Sabani Yanzu Tsakaninsa da Atiku

Rikicin PDP: Gwamna Ya Gyara Zance, Ya ce Babu Sabani Yanzu Tsakaninsa da Atiku

Bala Mohammed ya tabbatarwa mutanen jihar Bauchi cewa babu wata rigima da shi da Atiku Abubakar

Gwamna Mohammed yace rashin jituwar da aka samu tsakaninsa da Atiku ya wuce, yana goyon bayansa

Kauran Bauchi ya yi wannan bayani a gaban Uwargidar ‘dan takaran PDP a 2023, Hajiya Titi Abubakar

Bauchi - Mai girma gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed yana goyon bayan Atiku Abubakar ya zama shugaban Najeriya a karkashin jam’iyyar PDP.

Daily Trust ta ce Gwamna Bala Mohammed ya halarci taron da mai dakinsa, Aisha Bala Mohammed ta shirya na rabawa mata 3, 000 kayan yin sana’a.

Hajiya Aisha Bala Mohammed ta rabawa mata kaya dabam-dabam a filin wasa na Abubakar Tafawa Balewa da ke garin Bauchi a karshen makon jiya.

Uwargidar ‘dan takaran shugaban kasa na PDP, Hajiya Titi Atiku Abubakar ta halarci taron.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fi Shettima Lafiya, Rawar 'Buga' Da Yayi Alama ce, 'Dan Majalisar Wakilai Dambazau

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton ya ce a wajen taron ne Bala Mohammed ya fadawa Titi Atiku Abubakar ta sanar da maigidanta yana goyon bayan neman mulkin da yake yi.

Ki fadawa Atiku, muna tare - Bala ga Titi

"Uwarmu, ina mai tabbatar maki da cewa karyar banza ce mutane suke yi, su na cewa ba na tare da Atiku Abubakar; karya ce.
Na sabu sabani da yayanmu wanda da yardar Allah zai zama sabon shugaban kasar Najeriya, amma yanzu komai ya wuce.
Ko a fili ko a sirri, idan akwai wani wanda na taba fadawa cewa ba na goyon bayan Atiku Abubakar, sai ya fito fili ya fada."

- Gwamna Bala Mohammed

Atiku Abubakar
Atiku Abubakar a Kogi Hoto: @Atiku.org
Asali: Facebook

Hajiya Titi Atiku Abubakar ta tabbatarwa mutaen garin Bauchi cewa matasa da mata za su amfana sosai idan har aka yi dace mai gidanta ya hau ragamar mulki.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Bidiyo ya fito, Atiku ya dawo daga Landan tare da wasu jiga-jigan PDP

A zabi Atiku Abubakar - Gwamna Bala

Jaridar Sun ta ce Gwamnan ya yi kira ga mutanen jihar Bauchi da su zabi jam’iyyar PDP, ya ce ita kadai ce za ta iya ceto Najeriya daga halin da aka shiga ciki.

Da yake jawabi a garuruwan Gamawa da Zaki, Gwamnan Bauchi ya ce Atiku Abubakar ne ‘dan takaran da ya san mafitar matsalar tattalin arzikin kasa.

“Ku na bukuta ta kamar yadda nake bukatarku.”

Kun ji labarin yadda Bola Tinubu wanda shi ‘Dan takaran jam’iyya mai mulki ya zauna da ‘yan takaran APC a zabe mai zuwa a ranar Lahadi a Abuja.

A taron da aka yi, ‘dan takaran ya yi maganar shirye-shiryen zabe, ya ce ya zama dole wadanda suke takara APC su dage a zabe domin gudun a ji kunya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel