Kungiyoyin Kwadugo Sun Ayyana Goyon Bayansu Ga Bola Tinubu da Gwamnan APC

Kungiyoyin Kwadugo Sun Ayyana Goyon Bayansu Ga Bola Tinubu da Gwamnan APC

  • Kungiyoyin kwadugo a jihar Legas sun bayyana goyon bayansu ga kudirin Bola Ahmed Tinubu na zama shugaban kasa
  • Kungiyoyin sun kuma ce suna tare da burin gwamna Babajide Sanwo-Olu na tazarce a kujerarsa ta gwamnan jihar Legas
  • Sun bayyana matsayarsu ne a wurin ralin da suka shirya a kwalejin yan sanda dake Ikeja ranar Alhamis

Lagos - Kungiyoyin kwadugo a jihar Legas sun ayyana goyon bayansu ga burin Bola Ahmed Tinubu na zama shugaban ƙasa da gwamna Babajide Sanwo-olu na zarcewa a kujerarsa a 2023.

Jaridar Punch ta ce wannan ci gaban na kunshe ne a wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar Legas, Gbenga Omotosho, ya fitar ranar Alhamis 12 ga watan Janairu, 2023.

Bola Tinubu da Babajide Sanwo-Olu.
Kungiyoyin Kwadugo Sun Ayyana Goyon Bayansu Ga Bola Tinubu da Gwamnan APC Hoto: Bola Tinubu
Asali: Facebook

Kwamishinan ya sanar da cewa:

"Labari da zafinsa, Kungiyar kwadugo ta ayyana goyon baya da kudirin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu na zama shugaban kasa, da Babajide Sanwo-Olu mai neman zango na biyu a gangamin da ya gudana a Kwalejin yan sanda, Ikeja, jihar Legas."

Kara karanta wannan

Tashin Hankali Ga Atiku, Tinubu Ya Ziyarci Fitaccen Gwamnan G5, Bidiyo da Hotuna Sun Bayyana

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Bola Tinubu, tsohon gwamnan na tsawon zango biyu a jihar Legas, na neman zama shugaban kasa karkashin inuwar jam'iyyar APC mai mulki.

Tsohon gwamnan ya sha nanata cewa, "Yanzun lokaci na ne," bayan ya taka muhimmiyar rawa wajen kawar da jam'iyya mai mulki PDP a zaben 2015.

Yadda gangamin ma'aikatan ya gudana

Shugabar NLC a Legas, Funmilayo Sessi, da takwaranta na TUC, Kwamaret Gbenga Ekundayo, su ne suka jagoranci dubbannin ma'aikata a Ralin wanda ya gudana a kwalejin yan sanda, Ikeja.

Sessi ta yi bayanin cewa matakin da suka dauka ba wani shiri bane na maida kungiyoyin kwadugo na siyasa, kamar yadda jaridar PM News ta ruwaito.

Tace sun dauki matakin mara wa gwamna Sanwo-Olu baya ne bayan mambobinta ba tare da samun saɓani ba sun amince su goya masa baya bisa la'akari da cika alkawarinsa ga ma'aikata.

Kara karanta wannan

A Gaban Buhari a Yobe, Bola Tinubu Ya Faɗi Matakin da Zai Dauka Kan ASUU Idan Ya Ci Zaben 2023

Hotuna Da Bidiyo Sun Bayyana Yayin da Tinubu Ya Ziyarci Gwamnan G5, Ifeanyi Ugwuanyi

A wani labarin kuma Ana gab da zabe, Bola Tinubu ga ziyarci daya daga cikin gwamnonin G5 da suka ware kansu daga PDP

Dan takarar shugaban ƙasa a inuwar APC ya je har gidan gwamnatin jihar Enugu tare da gwamna Dave Umahi na jihar Ebonyi, sun tattauna da gwamna Ugwuanyi.

Ana zargin tsohon gwamnan jihar Legas din ya kulla yarjejeniya da tawagar G5 a wani taro da ake tsammanin ya gudana tsakaninsu a Landan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel