Yar Takarar Mataimakin Gwamna Ta Sauya Sheka Daga APC Zuwa PDP

Yar Takarar Mataimakin Gwamna Ta Sauya Sheka Daga APC Zuwa PDP

  • Saura kwanaki 49 zaben shugaban kasa na 25 ga watan Fabrairu, 2023, jam'iyar APC mai mulki ta shiga rudani a Kuros Riba
  • Tsohuwar yar takarar gwamnan jihar a zaben 2023, Helen Boco, ya sauya sheka zuwa PDP
  • A cewarta su ne suka sha wahala wurin kafa APC amma abun mamaki su aka maida saniyar ware

Cross River - Yar takarar mataimakin gwamnan jihar Kuros Riba karkashin APC a zaben 2019, Misis Helen Boco, ta fice daga jam'iyya mai mulki zuwa Peoples Democratic Party (PDP).

Jaridar Tribune Online ta rahoto cewaa an samu wannan ci gaban ne yayin da ya rage kwanaki 49 a fafata zaben shugaban kasa ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023.

Helec Boco.
Yar Takarar Mataimakin Gwamna Ta Sauya Sheka Daga APC Zuwa PDP Hoto: tribuneonline
Asali: UGC

A cewarta, duk da rawar da ta taka wurin gina APC tun asali, sai gashi shugabanni sun maida ita saniyar ware shiyasa ba zato ba tsammani ta koma PDP.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Hukumar NRC Ta Rufe Tashar Jirgin Kasa da Yan Bindiga Suka Kai Hari

A kalamanta ta ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Na raba gari da APC, kamar yadda kuke gani na yi rijista da PDP har katina ya zo hannuna jiya. Na ji dadin shiga sabuwar jam'iya, akalla dai an saurare ni kuma an ji kuka na."

Tsohuwar yar takarar gwamnan ta kara da cewa har zuwa ranar 6 ga watan Janairu, 2023 ta kasance mambar APC ta asali kuma da ita aka sha wahalar rainon jam'iyyar har ta ginu.

Premium Times ta rahoto yar siyadan ta ci gaba da cewa:

"Da ni aka gina APC har zuwa lokacin gwamna ya shigo, mun ji dadi saboda mulki ya dawo hannunmu amma a yanzu babu farin ciki a cikin APC."
"A shekarar da ta gabata na nemi shugabar matan APC ta kasa amma aka hana ni duk sadaukarwan nan da na yi."

Kara karanta wannan

Manyan Dalilai Uku da Zasu Ja Hankalin 'Yan Arewa Su Zabi APC a 2023, Gwamna

"A yanzu Atiku Abubakar ya dauko ni ya sanya ni a tawagar kamfe mai zaman kanta, na amince da haka, a shirye nake kuma nasan jama'a ma sun shirya don mara masa baya."

Dan Majalisar Kano Ya Yi Amai Ya Lashe, Ya Koma Jam'iyyar APC

A wani labarin kuma bayan sauya sheka zuwa NNPP, Dan Majalisar dokokin Kano ya yi amai ya lashe, ya sake komawa APC

Dan majalisa mai wakiltar Gwale a majalisar Kano, Yusuf Babangida, ya koma APC bayan barinta zuwa NNPP a baya.

Yace ya tsinci kansa a wani hali a cikin NNPP, lamarin ya sa ba shi da zabin da ya wuce ya tattara kayansa ya bar inuwar kayan marmari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel