Mataimakin Shugaban Kasa, da 'Yan APC 5 da Ba a Taba Gani Wajen Yakin Zabe ba

Mataimakin Shugaban Kasa, da 'Yan APC 5 da Ba a Taba Gani Wajen Yakin Zabe ba

  • Da alama har yanzu kura ba ta lafa a jam’iyyar APC ba tun bayan damkawa Bola Tinubu tikitin takara
  • Watakila wasu daga cikin wadanda suka nemi takarar kujerar shugabancin Najeriya a APC ba su huce ba
  • Akwai ‘yan APC da ya kamata a gani a sahun gaba-gaba, amma sun guji yawon kamfen da Tinubu yake yi

Mun tattaro wasu daga cikin jagororin jam’iyyar APC da ba a ganin duriyarsu a wajen yakin neman zaben Bola Tinubu.

1. Yemi Osinbajo

Tunda aka soma kamfe, mataimakin shugaban kasa watau Farfesa Yemi Osinbajo bai halarci yawon yakin neman zaben jam’iyyarsa ta APC ba.

Legit.ng ta lura bayan zaben gwani, Yemi Osinbajo da Bola Tinubu sun gana a fili sau biyu ne.

A 2015 da 2019, tsohon gwamnan na Ribas ne shugaban yakin takarar Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

Shekarau da Jiga-Jigan 'Yan siyasa 8 da Suka Tafka Asara 10 da 20 a Zaben Bana

2. Ogbonnaya Onu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani tsohon Minista kamar Rotimi Amaechi da ya guji harkokin APC a yau shi ne Dr. Ogbonnaya Onu, wanda ya nemi a ba shi tikitin takarar shugaban kasa na 2023.

Tinubu
Bola Tinubu a Yobe Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

Rahoton ya ce na-kusa da Onu sun nuna yana taka rawar gani a tafiyar Tinubu, amma a bayan-fage.

3. Chukwuemeka Nwajiuba

Tsohon karamin Ministan ilmi watau Chukwuemeka Nwajiuba yana cikin wadanda suka fi nuna gaba ga Bola Tinubu bayan ya sha kasa a zaben tsaida gwani.

Abin ya kai Hon. Nwajiuba ya shigar da kara a kotu, yana kalubalantar takarar Tinubu.

4. Rochas Okorocha

Babu abin da ya hada Sanatan Imo na yamma, Rochas Okorocha da yakin zaben APC domin bai cikin ‘yan kwamitin da aka zakulo su taya ‘dan takara kamfe.

Sai da Okorocha wanda ya dade yana burin zama shugaban kasa ya jaddada zamansa a APC.

Kara karanta wannan

Ana Neman Hana Tinubu Hawa Mulki, Atiku Ya Kinkimi Lauyoyi, An Garzaya Kotun Zabe

5. Tunde Bakare

Tunde Bakare yana cikin ‘yan kwamitin PCC da ke yi wa jam’iyyar APC yakin neman zaben shugaban kasa, amma za iyi wahala idan an taba ganin keyarsa.

Bakare jagora ne a APC, da shi Muhammadu Buhari ya yi takara a CPC a zaben 2011.

Tazarcen Gwamnan Bauchi

Tsohon Wazirin Bauchi ya fito yana cewa yayi wa Bala Mohammed riga da wando domin ya zama Gwamna a 2019, sai ya juya masu baya da ya hau mulki.

An ji labari Muhammadu Bello Kirfi ya yi kaca-kaca da Bala Mohammed, ya ce tun da aka tube masa sarauta, Gwamnan ba zai samu tazarce a jihar Bauchi ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel