Basaraken da Aka Tubewa Rawani Ya Ja Daga, Ya Rantse Sai Ya Hana Gwamna Tazarce a PDP

Basaraken da Aka Tubewa Rawani Ya Ja Daga, Ya Rantse Sai Ya Hana Gwamna Tazarce a PDP

  • Alhaji Muhammadu Bello Kirfi ya yi magana a kan sauke shi da aka yi daga sarautar Wazirin Bauchi
  • Tsohon Wazirin Bauchi yana mai da-na-sanin taimakawa Bala Mohammed wajen zama Gwamna a 2019
  • Dattijon ya fadawa manema labarai bai damu da cire masa rawani ba, ya ce Bala zai bar gidan gwamnati

Bauchi - Tsohon Wazirin Bauchi, Muhammadu Bello Kirfi, ya ce zai sauke Bala Mohammed daga kan kujerar Gwamna kamar yadda ya daura shi a mulki.

A ranar Litinin, 9 ga watan Junairu 2022, Daily Trust ta rahoto martanin da Muhammadu Bello Kirfi ya yi bayan sauke shi daga kujerar Wazirin Bauchi.

Da ya zanta da manema labarai a gidansa da ke garin Bauchi, an ji tsohon Wazirin ya na cika-bakin cewa Sanata Bala A. Mohammed zai bar matsayin Gwamna.

Kara karanta wannan

Yadda Shugaban Kasa Ya Tsira Daga Yunkurin Tsige Shi a Majalisar Dattawa – Sanatan PDP

Rahoto ya zo cewa Kirfi ya ce tun farko bai so ya karbi sarautar Wazirin Bauchi ba domin albashin bai kai abin da yake samu daga kasuwanci da siyasarsa ba.

Mu ne muka kawo Bala A. Mohammed - Kirfi

Yadda na kawo shi ofis, haka zai bi ya bar kan karagar mulki. Nayi nadamar abin da ya faru domin ya dade yana damu na a rai na.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ina cikin wadanda suka tsaya masa har ya zama Gwamna, sai ban ji dadin abin da ya faru ba.
Gwamnan PDP
Gwamna Bala Mohammed Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC
Iyakar abin da zai iya yi mani kenan, amma hakan bai da tasiri domin babu abin da nake samu da sarautar Waziri a fadar Sarki.
Na taka rawar gani wajen daura shi mulki a 2019. A lokacin da Bala yake neman cin ma burin siyasarsa, na yi masa komai.

Kara karanta wannan

Rikicin Tinubu da Ministan Buhari: An Bukaci Minista Ya Durkusa, Ya Ba Tinubu Hakuri Komai Ya Wuce

Nayi duk abin da zan iya wajen ganin ya kifar da gwamnatin da ke da goyon bayan gwamnatin tarayya a wancan lokacin.

- Muhammadu Bello Kirfi

Bala ya ci amanar mutanen Bauchi?

A cewar tsohon Wazirin, Gwamnatin PDP ta Bala ta gagara cika alkawuran da tayi wa mutanen jihar, a karshe ta koma yakar duk wadanda suka taimake ta.

Sun ta rahoto Kirfi yana cewa Bala Mohammed ya yi watsi da gudumuwar da manyan ‘yan siyasa suka ba shi wajen ganin ya zama Gwamnan Bauchi.

A karshe, tsohon Wazirin ya ce zai bar komai ga Allah madaukaki domin ya yi masu hisabi.

Dalilin cirewa Waziri rawani

A baya an ji yadda Alhaji Muhammadu Bello Kirfi ya rasa sarautar Wazirin Bauchi da matsayin ‘Dan majalisa a fadar Sarki bayan samun sabani da Gwamnansa.

Masarautar Bauchi a karkashin jagorancin Sarki Rilwanu Suleiman Adamu, ta nada Muhammad Uba Ahmed Kari a matsayin Wazirinta bayan abin da ya faru.

Kara karanta wannan

Fasto Ya Rabu da Harkar Addini, Ya Fito Neman Gwamna Gadan-Gadan a Jam’iyyar APC

Asali: Legit.ng

Online view pixel