Kuri'un APC a Arewa Suna Nan a Killace, Kwankwaso da Obi Mu Suke Wa Aiki, Sanata

Kuri'un APC a Arewa Suna Nan a Killace, Kwankwaso da Obi Mu Suke Wa Aiki, Sanata

  • Sanata Orji Kalu na jam'iyar APC ya yi ikirarin cewa Kwankwaso da Obi suna wa Tinubu aiki ba su sani ba
  • Kalu, tsohon gwamnan jihar Abiya yace Bola Ahmed Tinubu ne zai lashe zabe mai zuwa yayin da Atiku zai zo na biyu
  • A cewarsa har yanzun yankunan da suke tushen samun kuri'un APC na nan a killace amma sauran kawuna sun rabu

Mai ladabtarwa a majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Orji Kalu, yace kuri'un jam'iyyar APC na arewa maso yamma da arewa maso gabashin Najeriya na nan a killace.

Sanatan ya kuma yi ikirarin cewa Rabiu Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa a NNPP da takwaransa na LP, Peter Obi, na aiki domin nasarar Bola Tinubu ne ta hanyar raba kuri'un yan kudu.

Orji Kalu.
Kuri'un APC a Arewa Suna Nan a Killace, Kwankwaso da Obi Mu Suke Wa Aiki, Sanata Hoto: Orji Kalu
Asali: UGC

Kalu, tsohon gwamnan jihar Abiya ya yi wannan furucin ne a gidan Talabijin din Channels tv cikin shirinsu mai suna, Political Paradigm, wanda ake watsawa ranar Talata.

Kara karanta wannan

An Tono Babban Abinda APC Ta Rasa a Arewa Wanda Zai Ja Wa Tinubu Shan Kaye a Zaben 2023

Jigon APC mai mulki yace bai yarda da zabukan gwajin da ake shiryawa kafin zabe ba, wnada ya dora Peter Obi a kan sauran masu neman shugaban kasa 18 ciki har da Tinubu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kalu ya ce:

"Ban yarda da irin zaben nan na gwaji ba, ba gaskiya bane. Idan ana son kwatanta gaskiya, Kwankwaso da Obi mu suke wa aiki saboda babu wanda ya taba tushen kuri'unmu."
"Babu wanda ya taɓo sansanin APC mai karfi, arewa maso yamma da arewa maso gabas nan ne asalin sansanin da APC ke da karfi. Amma idan ka zo kudu maso gabas da kudu-kudu duk an rarrabu, zancen Obideint ake."
"Ba wanda ya shiga shiyyoyin da muke da karfe, komai na nan yadda yake a tushen masoyan mu, yana nan yadda yake da kyau."

Tsohon gwamnan Abiya yace dan takarar shugaban kasa a inuwar APC, Bola Tinubu ne zai zama magajin Buhari a 2023 yayin da takwaransa na PDP, Atiku Abubakar zai zo na biyu.

Kara karanta wannan

2023: Tinubu Ya Dauki Babban Alkawari a Gaban Buhari a Yola, Ya Raɗa Wa PDP Sabon Suna

Jam'iyar APC Ta Rasa Kaso 70 Na Magoya Bayanta a Arewa, Jibrin

A wani labarin kuma Tsohon dan majalisar tarraya ya ce APC ta rasa kaso 70 na kuri'un da take samu a arewacin Najeriya

Abdulmumin Jibrin, kakakin kamfen NNPP yace yan arewa kaso 70 zuwa 80 cikin Ɗari sun dawo daga rakiyar jam'iyyar APC.

Tsohon dan majalisar yace Kwankwaso zai kwashe dukka kuri'un arewa ya tsakuro na kudu kuma ya yi nasara a zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262