NNPP Ta Bayyana Abin da Kwankwaso Yake Yi da Ya Sha Gaban Atiku, Tinubu da Obi

NNPP Ta Bayyana Abin da Kwankwaso Yake Yi da Ya Sha Gaban Atiku, Tinubu da Obi

  • Abdulmumin Jibrin yana ganin idan ana maganar yawon kamfe, babu kamar Rabiu Musa Kwankwaso
  • Kakakin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasan NNPP ya ce Kwankwaso ya leka garuruwan 400
  • Dr. Jibrin ya ce a sauran masu neman takaran shugabancin Najeriya, babu wanda ya iya shiga jihohi 18

Abuja - Saura kwanaki 46 a shiga filin zabe, amma sai yanzu Rabiu Musa Kwankwaso ya rantsar da kwamitin yakin zama shugaban kasa.

Wannan ce tambayar da bijirowa Abdulmumin Jibrin a gidan talabijin Channels TV a ranar Litinin da aka yi hira da shi a kan shirin jam’iyyarsu ta NNPP.

Dr. Abdulmumin Jibrin ya nuna rantsar da kwamitin ba shi ne ba, domin tun tuni NNPP da ‘dan takararta suke yawon kamfe domin samun nasara.

Tsohon ‘dan majalisar tarayyar yake cewa tun kafin ‘yan takaran APC, PDP da LP su ankara, Sanata Rabiu Kwankwaso yake zagaye daga gari zuwa gari.

Kara karanta wannan

Da Dumi-duminsa: Hoton Atiku Cikin Murmushi Ya Bayyana Yayin da Ake Rade-radin Bai Da Lafiya

Tun tuni muke aiki - Jibrin

Kakakin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasar ya ce sun yi ta zama da jama’a, da haduwa da ‘yan jam’iyya da bude ofishin NNPP a Najeriya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An rahoto Jibrin yana cewa wadanda aka sa a kwamitin yakin takarar na-kusa da Kwankwaso ne wadanda aka yi tafiya da su daga TNM zuwa NNPP.

NNPP.
Kwankwaso ya rantsar da kwamitin yakin neman zabe Hoto: @SaifullahiHon
Asali: Twitter

“Idan mutane suka ga labarai a yau za su je sai yanzu suke kafa kwamitin yakin neman zabe, a zahiri kwamitin yana ta yin aiki tun tuni.
Sai yanzu ne ake tabbatar da kwamitin da sunan rantsarwa, yana da muhimmanci ayi duk abin da ake yi, amma mun dade ana aiki.”

- Dr. Abdulmumin Jibrin

NNPP za ta zo bayan APC, PDP da LP?

Har ila yau da aka yi masa tambaya game da hasashen da wasu ke yi cewa NNPP za ta zo ta hudu a zaben bana, Hon. Jibrin ya ce ba haka abin yake ba.

Kara karanta wannan

Rigingimun PDP: Daga Karshen Atiku Ya Sake Rokon Gwamnanonin G5

‘Dan siyasar ya ce Sanata Kwankwaso ya nuna abin ban mamaki da ya dauko jam’iyya kuma yake yakin neman mulkin Najeriya a watanni kadan.

A bangaren kamfen, ya fi kowane ‘dan takara kokari nesa ba kusa ba. Ba jihohi yake zuwa ba, babu ‘dan takaran da ya shiga ko da rabin jihohin Najeriya.
Amma Kwankwaso ya ziyarci kananan hukumomi fiye da 400, wannan na nan a rubuce. An fitar da bidiyo yau, za a ga kauyuka da garuruwan da ya shiga.

A bidiyon, za a ji jigon na NNPP yana cewa ‘dan takaransu zai iya zagayawa duka kananan hukumomi 774 da ake da su kafin lokacin da za a rufe kamfe.

- Dr. Abdulmumin Jibrin

Meyasa Obasanjo ya bi LP?

Rahoto ya zo cewa Mahdi Shehu ya ce Obasanjo ya kakaba Ummaru Musa ‘Yar’adua da Dr. Goodluck Jonathan ne saboda ya dauka zai juya su a kan mulki.

Kara karanta wannan

Ana Zanga-Zanga, ‘Yan APC Sun Tada Rigima kan Zargin Shugabanni da Satar $1.5m

‘Dan kasuwar ya ce a dalilin irin haka Obasanjo yake goyon bayan Peter Obi ya karbi mulki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel