'Yan Bindiga Sun Kai Hari Babban Ofishin Kamfen Tinubu a Jihar Osun

'Yan Bindiga Sun Kai Hari Babban Ofishin Kamfen Tinubu a Jihar Osun

  • Wasu miyagu dauke da bindigu da makamai masu hadari sun kai hari Ofishin kamfen Tinubu/Shettima a jihar Osun
  • Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun tafka ta'asa a harin, sun lalata allunan sanarwa, kofofi da gilasan tagogi
  • Lamarin dai ya faru ne awanni kadan bayan tsohon gwamnan jihar, Oyetola ya kai ziyara domin duba Ofishin a Ilesha

Osun - Wasu miyagun 'yan bindiga sun kai farmaki babban Ofishin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa a inuwar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, a jihar Osun.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa lamarin ya auku ne awanni kalilan bayan tsohon gwamnan jihar, Adegboyega Oyetola, ya kai ziyarar gane wa idonsa a Ofishin da ke Ilesha.

Harin Ofishin kamfe a Osun.
'Yan Bindiga Sun Kai Hari Babban Ofishin Kamfen Tinubu a Jihar Osun Hoto: thenation
Asali: UGC

Bayanai sun nuna cewa maharan sun mamaye Ofishin da misalin karfe 9:30 na safe dauke da bindigu, Adduna da sauran makamai masu haɗari.

Kara karanta wannan

Edo: 'Yan Bindiga Sun yi Garkuwa da Shugaban Alkalan Kotun Gargajiya ta Jihar

Yan bindigan sun yi kaca-kaca da kayayyakin Ofishin

Legit.ng ta gano cewa yan bindigan sun lalata Allunan da aka liƙa fastoci a Ofishin, sun farfasa kofofi da gilasan Tagunan wurin baki ɗaya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Tsohon kwamishinan ayyuka da sufuri a jihar Osun a zamanin gwamnatin da ta shude, Remi Omowaye, ya ayyana harin da aka kai Ofishin kamfen Tinubu/Shettima da aikin sheɗanci

Wannan na zuwa ne makonni bayan gwamna Oyetola ya koma jihar Osun tun bayan mika mulki ga sabuwar gwamnati ta gwamna Ademola Adeleke na PDP.

A wani taro da jagororin APC suka shirya domin dawowarsa, Gwamna Oyetola yace wannan shekarar da aka shiga 2023 zata zo da manyan abubuwa biyu.

A cewarsa, Allah ya gaya masa cewa Bola Tinubu zai zama shugaban ƙasa kuma zai kwato hakkinsa ya koma kujerar gwamnan Osun bayan shan kasa a zaben watan Yuli.

Kara karanta wannan

2023: Ana Jiran Jin Wanda G5 Zasu Goyi Baya, Sabuwar Rigima Ta Bullo PDP a Arewacin Najeriya Kan Atiku

NNPP mai kayan marmari zata fara kamfen 2023

A wani labarin kuma Tsohon gwamnan Kano, Kwankwaso Ya Bayyana Kwamitin Yakin Neman Zaben NNPP 2023

Bayan dogon lokaci, Kwankwaso ya kaddamar da mambobin tawagar yakin neman zaben shugaban kasa na NNPP mai kayan dadi a Abuja yau.

Kwankwaso ya yi kira ga 'yan Najeriya musamman mambobin NNPP da kungiyoyin magoya baya da su hada hannu da kwamitin don gina sabuwar Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel