Kwankwaso Ya Bayyana Kwamitin Yakin Neman Zaben NNPP 2023

Kwankwaso Ya Bayyana Kwamitin Yakin Neman Zaben NNPP 2023

  • Mai neman zama shugaban kasa a inuwar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, ya kaddamar da kwamitin kamfe a Abuja
  • Tsohon gwamnan jihar Kano ya yi kira da daukacin Yan Najeriya su hada hannu da PCC na NNPP domin gina sabuwar Najeriya
  • Kwankwasso na daga cikin manyan 'yan takara hudu da ake ganin dayansu ne zai gaji shugaba Buhari a watan Mayu

Abuja - Dan takarar shugaban kasa a inuwar jam'iyar NNPP mai kayan dadi, Rabiu Kwankwaso, ya kaddamar da kwamitin kamfen shugaban kasa (RMK, PCC).

Da yake jawabi ga magoya bayan NNPP a Abuja ranar Litinin (yau), Kwankwaso, yace NNPP na aiki ba dare ba rana domin fara yakin neman zabe na gina sabuwar Najeriya daga 29 ga watan Mayu, 2023.

Rabiu Musa Kwankwaso.
Kwankwaso Ya Bayyana Kwamitin Yakin Neman Zaben NNPP 2023 Hoto: @honsaifullahi
Asali: Twitter

A rahoton jaridar Vanguard, Tsohon gwamnan jihar Kano ya ce:

Kara karanta wannan

2023: Ana Jiran Jin Wanda G5 Zasu Goyi Baya, Sabuwar Rigima Ta Bullo PDP a Arewacin Najeriya Kan Atiku

"Da sunan Allah mai rahma mai jin kai, ina mai kaddamar da kwamitin RMK 2023 na kamfen shugaban kasa RPK-PCC domin amfanuwar 'yan Najeriya da kuma sha'awar gina sabuwar Najeriya."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ina kira 'yan Najeriya musamman mambobin jam'iyyar NNPP da kungiyoyin magoya baya da su hada hannu da kwamitin PCC da dukkan kwamitocin dake kunshe."

Yadda zamu fara kamfe a fadin Najeriya - Kwankwaso

Dan takarar shugaban kasan ya kuma kara da bayanin jihar da jirgin yakin neman zaben NNPP zai fara sauka da kuma gayyatar da gwamnatin Birtaniya ta masa.

"Ina farin cikin sanar muku cewa daga ranar 12 ga wannan watan (Janairu) zamu fara Ralin shiyyar arewa maso gabas a jihar Bauchi, arewa maso yamma a Kaduna ranar 14 ga wata da arewa ta tsakiya a Lafiya ranar 16 ga wata."
"Zamu daga gangamin kamfen na yan kwanaki domin samar da lokacin amsa gayyatar da Chatham House na Birtaniya suka mana inda zamu gabatar da kunshin manufofin mu ga duniya."

Kara karanta wannan

Magana Ta Kare: Shin Dagaske An Garzaya da Atiku Abubakar Asibiti Neman Lafiya? Gaskiya Ta Bayyana

"Muna dawowa daga Birtaniya zamu dora daga inda muka tsaya sannan mu karisa sauran shiyyoyin da bamu je ba."

- Rabiu Kwankwaso.

Rigima ta dauki sabon salo a PDP

A wani labarin kuma Rikici ya kara tsananta yayin da Tsagin Shema Na PDP a Jihar Katsina Sun Fara Kamfen Atiku Abubakar

Rigingimun PDP reshen Katsina sun kara tsananta, tsagin tsohon gwamna, Ibrahim Shehu Shema, sun ware suna tallata Atiku.

Majigiri, wanda ya jagoranci gangamin kamfen a Katsina, yace Atiku ya san wadan da ke tare da shi. Yakubu Lado ma yana na shi kamfe din daban.

Asali: Legit.ng

Online view pixel