Tsagin Shema Na PDP a Jihar Katsina Sun Fara Kamfen Atiku Abubakar

Tsagin Shema Na PDP a Jihar Katsina Sun Fara Kamfen Atiku Abubakar

  • Yayin da ake fama da rikicin gwamnonin G5, rigingimun PDP reshen Katsina ya kara tsananta a baya-bayan nan
  • Bayan darewar jam'iyyar gida biyu, tsagin Shema a PDP sun fara shirya kamfe na daban domin tallata Atiku kadai
  • Haka nan kuma bangaren dan takarar gwamna, Yakubu Lado, sun fara kamfen zaben watan Fabrairu

Katsina - Tsagin jam'iyyar PDP da ke goyon bayan tsohon gwamnan jihar Katsina, Ibrahim Shehu Shema, a ranar Lahadi sun gunar da gangamin kamfen Atiku Abubakar.

Ralin kamfe ɗin ya gudana ne karkashin jagorancin tsohon shugaban PDP reshen Katsina, Salisu Majigiri, wanda kuma ya wakilci Shema a wurin, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Atiku a Katsina.
Tsagin Shema Na PDP a Jihar Katsina Sun Fara Kamfen Atiku Abubakar Hoto: @atiku
Asali: Twitter

Shugabannin PDP daga dukkanan kananan hukumomi 34 da ke faɗin Katsina sun halarci taron kamfen ɗin wanda ya gudana a gaban Ofishin PDP da ke kusa da Rukunin gidajen Fagachi a birnin Katsina.

Kara karanta wannan

Da Dumi-duminsa: Hoton Atiku Cikin Murmushi Ya Bayyana Yayin da Ake Rade-radin Bai Da Lafiya

Da yake jawabi a wurin taron, Majigiri yace an shirya taron ne domin wayar da kan Katsinawa su zabi dan takarar shugaban kasa a inuwar PDP, Atiku Abubakar a zabe mai zuwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majigiri ya kara da cewa tsohon mataimakin shugaban kasa zai samu nasara a Katsina, ya kara da cewa rabuwar kan da aka samu a PDP ta jihar matsala ce ta shugabanci.

A cewarsa, rugimar shugbancin dake faruwa a jam'iyar ta Katsina ba zata shafi damar Atiku a zaben watan Fabrairu ba.

A kalamansa ya ce:

"Mun taru anan ne mu yi wa shugaban kasar mu kamfe, mun taru ne domin dan takarar mu, Atiku Abubakar. Ina tabbatar maku Atiku zai samu nasara a Katsina, ya san su wa ke tare da shi kuma ya san muna bayansa."
"Shiyasa shugabanmu mai girma tsohon gwamna, Barista Ibrahim Shema, yake kokarin ganin Atiku ya samu nasara a babban zabe, zamu ci gaba da shirya taruka dominsa kuma mun san da ikon Allah zai yi nasara."

Kara karanta wannan

Magana Ta Kare: Shin Dagaske An Garzaya da Atiku Abubakar Asibiti Neman Lafiya? Gaskiya Ta Bayyana

"Katsinawa zasu saka wa PDP bisa dumbin ayyukan da ta masu kuma su dangwala wa dan takarar mu na shugaban kasa idan zabe ya zo."

Legit.ng Hausa ta tuntubi Umar Idris Dabai, jigon PDP a karamar hukumar Danja kuma makusancin dan takarar majalisar tarayya a 2023, Abdullahi Balarabe Dabai, yace akwai babbbar matsala a PDP ta Katsina.

Umar ya shaida wa wakilin mu cewa game da dan takarar shugaban kasa kai a haɗe yake, amma Shema ya ware kansa yana takun saka da dan takarar gwamna, Yakubu Lado.

"Akwai matsala mai girma a PDP ta Katsina kuma idan ba'a dauki mataki ba zata haifar da abu mara kyau musamman a zaben gwamna. Shema ya ware baya tare da Yakubu Lado."

"Na san kun samu labarin gangamin Atiku na nan Katsina, na je wurin amma kusoshin PDP masu rike da manyan mukamai a jiha ba su halarta ba, dole a zauna a dinke baraka tun wuri," inji shi.

Kara karanta wannan

Ka yi hakuri, ba zan ba da ba: Gwamnan PDP a Arewa ya hana Buhari filin kamfen

Lafiyar Atiku kalau - Ibe

A wani labarin kuma Gaskiya ta bayyana game da raɗi-radin dake yawo cewa an garzaya da Atiku neman lafiya a kasar waje

Ana ta mahawara a kafafen sada zumunta kan inda dan takarar PDP, Atiku Abubakar, ya shiga aka daina jin duriyarsa, wasu na zargin ba shi da lafiya. Paul Ibe, mai magana da yawunsa yace Atiku ya tafi Dubai hutu, yau zai wuce Landan. Dino Melaye ya bayyana abinda ya kai Atiku kasar Birtaniya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel