Gwamnatin Adamawa Ta Hana Shugaba Buhari Amfani da Filin Taro a Shirin Gangamin Tinubu a Jihar

Gwamnatin Adamawa Ta Hana Shugaba Buhari Amfani da Filin Taro a Shirin Gangamin Tinubu a Jihar

  • Ahmad Fintiri, gwamnan jihar Adamawa ya hana shugaban kasa Muhammadu Buhari amfani da filin taron kamfen a jihar
  • Wannan na fitowa ne daga watawasikar da gwamnan ya kaiwa Buhari ta hannun sakataren gidan gwamnati, Bashiru Ahmad
  • Gwamnatin jihar Adamawa, wacce ta PDP ce ta bayyana dalilin da yasa ba za ta ba da filin taron ba don yin kamfen APC

FTC, Abuja - Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa ya ki amincewa da bukatar shugaban kasa Muhammadu Buhari na amfani da filin taro na Ribadu Square da ke jihar don kaddamar da kamfen APC a jihar.

Wannan na fitowa ne daga cikin wata takardar da gwamnan ya aikewa Buhari tare da sa hannun sakataren gidan gwamnati, Bashiru Ahmad, kamar yadda Legit.mg ta samo.

Wasikar ta bayyana dalilai da suka sa gwamnatin Adamawa ba za ta samu damar ba da filin taron ba, inda tace ana kan wannan babban aikin gyara a cikinsa.

Kara karanta wannan

2023: Magana Ta Kare, Wike da Ortom Sun Hada Baki, Sun Yi Magana Kan Dan Takarar da G5 Zata Marawa Baya

Gwamnatin Adamawa ta hana Buhari filin taron kamfen Tinubu
Gwamnatin Adamawa Ta Hana Shugaba Buhari Amfani da Filin Taro a Shirin Gangamin Tinubu a Jihar | Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

Ana kyautata zaton adawa ce ta hana ba da filin

Idan baku manta ba, ‘yar takarar gwamnan APC a jihar, Aisha Dahiru Ahmed (Binani) ce ‘yar takawar gwamna mace a manyan jam’iyyun siyasa na Najeriya guda biyu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta tsaya takara ne domin kalubalantar Fintiri a zaben 2023 mai zuwa, wanda shi kuma gwamnan PDP ne kuma jigonta a jihar da ke Arewa maso Gabas.

Shugaban kasa Muhammadu, a bangare guda, zai halarci taron gangamin na APC a jihar Adamawa a ranar Litinin mai zuwa, amma wasikar ta zo ba yadda ake so ba daga gwamnatin Adamawa.

Jihar Adamawa dai ta PDP ce, kuma dan takarar shugaban kasan PDP, Atiku Abubakar daga jihar ya fito.

Abin da wasikar ke cewa

Wasikar ta gwamna Fintiri ta ba shugaban kasa hakuri tare da bayyana masa dalilin da yasa ba za a iya ba da filin ga taron APC ba.

Kara karanta wannan

An ramawa Atiku: Gwamna mai ci da 'yan takarar gwamna 2 sun ki halartar kamfen PDP

Gwamnatin jihar ta ce, tuni an kwaba filin taron da kayayyakin ayyuka da a halin yanzu aka yi, don haka bai dace da taron da shugaban kasa zai halarta ba.

Ba wannan ne karon farko da ake samun tsaiko daga ‘yan siyasa ba, an sha yin hakan a wurare daban-daban a Najeriya.

Taron Kano Ya Tabbatar da Cewa Tinubu Ba Shi da Wani Abin da Zai Tsinanawa ’Yan Najeriya, Cewar Atiku

A wani labarin, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya caccaki Tinubu, ya ce dan takarar na APC ba zai tsinanawa Najeriya komai ba.

Ya fadi hakan ne bayan da jam’iyyar APC ta gudanar da taron gangaminta a jihar Kano, Arewa maso Yammacin Najeriya.

An ga Tinubu na tikar rawa a wurin taron gangamin na APC, mutane da yawa sun yi martani mai daukar hankali.

Asali: Legit.ng

Online view pixel