2023: Zamu Shugabanci Najeriya Tare da Jin Tsohon Allah, Peter Obi

2023: Zamu Shugabanci Najeriya Tare da Jin Tsohon Allah, Peter Obi

  • Mai neman zama shugaban kasa a inuwar Labour Party, Peter Obi, yace zai ji tsorom Allah idan aka zabe shi a zabe mai zuwa
  • A gangamin kamfensa na jihar Osun, Obi ya roki 'yan Najeriya su duba kwarewa da gogewa wajen zaben shugabanni na gaba
  • Tsohon gwamnan ya caccaki manyan jam'iyyun da suka mulki Najeriya da cewa su ne suka lalata tattalin arzikin kasa

Osun - Peter Obi, dan takarar shugaban kasa a inuwar Labour Party, yace idan ya zama shugaban kasa, gwamnatinsa zata shugabanci kasar nan tare da jin tsoron Allah.

Jaridar The Cable ta rahoto cewa Obi ya yi wannan furucin ne a wurin gangamin kamfen shugaban ƙasa na LP da ya guda a Osogbo, babban birnin jihar Osun.

Peter Obi.
2023: Zamu Shugabanci Najeriya Tare da Jin Tsohon Allah, Peter Obi Hoto: Peter Obi/facebook
Asali: Facebook

Tsohon gwamnan jihar Anambra ya roki daukacin 'yan Najeriya su zabi shugabanni masu gogewa da kwarewa, kar su yarda kabilanci ko Addini ya yi tasiri a kansu.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Tinubu Ya Caccaki Obasanjo da Atiku Ya Tono Zunubinsu Na Baya

Dan takarar LP yace shi da abokin gaminsa, Datti Baba-Ahmed sun shirya tsaf domin haɓaka tattalin arzikin Najeriya, ya kara da cewa sun kasance fitattun yan kasuwa ƙafin su tsunduma cikin siyasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Obi yace duk tsarukan da manyan jam'iyyu wadan da suka mulki kasar nan suka zo da shi ba abinda ya haifar sai tabarbarewar ci gaban kasa.

A kalamansa ya ce:

"Mutane na fama da yunwa, matasa basu da aiki sai zaman kashe wando, ba bu tsaro a hanyoyin Najeriya, duk waɗan nan kalubalen sun bullo ne a mulkin jam'iyun dake babatun suna da manufa mai kyau."
"Amma tsarukansu ne suka lalata Najeriya, ina son da ni da ku mu tashi mu ruguza wadan nan tsaruka ta hanyar buga su da ƙasa a zaben wata mai zuwa Zamu dawo da tsaro da haɗin kan kasa."

Kara karanta wannan

Manyan Dalilai Uku da Zasu Ja Hankalin 'Yan Arewa Su Zabi APC a 2023, Gwamna

"Zamu jagorance ku cikin jin tsoron Allah, zamu bude muku kofar samun aiki, zamu sauya Najeriya daga mai dogara da kayan waje zuwa mai samarwa da fitar da kayayyaki kasashen waje."

Wasu Shugabannin APC Na Yi Wa Atiku Aiki a Akwa Ibom, Sanata Akpabio

A wani labarin kuma Babban jigon jam'iyyar APC a kasa ya yi zargin wasu daga cikin jagororin APC a jihar Akwa Ibom na yi wa PDP aiki

Tsohon ministan Buhari kuma mataimakin shugaban kwamitin kamfen APC na kasa, Godswill Akpabio, yace wasu jiga-jigai suna yi wa Atiku aiki a boye.

Sanatan ya ce ya san wasu shugabannin APC a jihar ta Akwa Ibom, wadanda ke fadin Sai Asiwaju da rana amma da daddare su koma Atiku da PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel