Ina Atiku Yake? Ya Sake Zuwa Dubai Kanin Likita, Kafarsa Na Ciwo: Fani Kayode

Ina Atiku Yake? Ya Sake Zuwa Dubai Kanin Likita, Kafarsa Na Ciwo: Fani Kayode

  • Wani Jigon jam'iyyar All Progressive Congress (APC), Femi Fani-Kayode ya caccaki dan takaran shugaban kasa PDP
  • Wannan ya biyo bayan jita-jitan dake yaduwa cewa an nemi Atiku an rasa kuma ba ya Najeriya
  • Fani Kayode wanda tsohon ministan sufurin jirgin sama ne yace Atiku ya tafi Dubai ganin Likita

Diraktan ayyuka na musamman da kuma sabbin kafafen yada labarai na kwamitin kamfen Tinubu/Shettima, Femi Fani-Kayode, ya bayyana inda dan takarar kujerar shugaban kasan PDP, Atiku Abubakar, ya shiga.

Fani Kayode yace Atiku fa ba lafiya gareshi ba kuma ya tafi kasar Dubai a dinke masa kafarsa dake masa ciwo.

Ya bayyana hakan ne a jawabin da ya fitar ranar Lahadi, 8 ga Junairu a shafinsa na Tuwita kuma Legit ta gani.

Fani ky
Ina Atiku Yake? Ya Sake Zuwa Dubai Kanin Likita, Kafarsa Na Ciwo: Fani Kayode
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Tinubu Ya Caccaki Obasanjo da Atiku Ya Tono Zunubinsu Na Baya

Fani Kayode wanda tsohon abokin Atiku ne a PDP ya ce Atiku zai garzaya Landan daga Dubai bayan ganin Likitansa.

Yace:

"Kuma dai, mutumin da ke son sayar da komai ya fadi rashin lafiya kuma ya gudu Dubai ayi masa aikin Tiyata. Ku lura da yadda yake tafiya zaku fahimci abinda ke faruwa da shi."
"Yanzu yana hanyar tafiya UK don ganin yan majalisan dokokin Birtaniya."

Jawabin Fani Kayode ya biyo bayan jita-jitan da ya yadu a kafafen sada zumunta cewa an kwana biyu ba'a ga a taruka na siyasa ba.

Abokan hamayyarsa, Bola Tinubu, na APC da Peter Obi na LP suna cigaba da yawon yakin neman zabe amma Atiku shiru.

Yanzu ana saura wata daya da yan kwanaki a gudanar da zaben shugaban kasan Najeriya wanda zai gaji shugaba Muhammadu Buhari.

Zaben shugaban kasan zai gudana ne ranar 28 ga watan Febrairu, 2023.

Kara karanta wannan

Ai sai dai rawan: Atiku ya ce Tinubu ba zai iya yiwa 'yan Najeriya komai sai abu 1

Asali: Legit.ng

Online view pixel