Ma’aikatan Najeriya Sun Ayyana Wadanda Za Su Zaba Daga Sama Har Kasa a 2023

Ma’aikatan Najeriya Sun Ayyana Wadanda Za Su Zaba Daga Sama Har Kasa a 2023

  • Idan zabe ya zo, ma’aikatan Najeriya duk za su hadu ne su dangwalawa Peter Obi ya karbi mulki
  • Shugaban kungiyar NLC, ya ce su na goyon bayan LP a zaben shugaban kasa da sauran kujeru
  • Ayuba Wabba ya shaidawa al’umma cewa kungiyar da yake jagoranta tana tare da takarar Obi

Abuja - Kungiyar kwadago ta kasa watau NLC ba ta tare da wadanda ake ganin su ne manyan ‘yan takarar shugabancin Najeriya a zabe mai zuwa.

Kungiyar NLC za ta mara baya ga Peter Obi mai takarar kujerar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar LP, The Nation ta fitar da rahoton nan.

Shugaban kungiyar na kasa, Kwamred Ayuba Wabba ya shaida cewa ma’aikatan Najeriya za su goyi bayan duk wani wanda ya tsaya takara LP.

Tun fil azal an kafa jam’iyyar LP ne domin ‘yan kwadago, daga baya ne aka bar kofa a bude har ta kai ‘yan siyasa su na rajista domin su shiga takara.

Kara karanta wannan

Yadda Shugaban Kasa Ya Tsira Daga Yunkurin Tsige Shi a Majalisar Dattawa – Sanatan PDP

LP ta ma'aikata ce har gobe

Da The Nation tayi hira da shi, Kwamred Wabba ya ce ma’aikata suke da jam’iyyar hamayya ta LP har gobe, kuma saboda ma’aikata aka kafa ta.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Mu ne muke da jam’iyyar Labour Party, sannan muna masu bada cikakkiyar goyon baya ga duka ‘yan takaranmu.

- Peter Obi

Peter Obi
Magoya bayan Peter Obi a Osun Hoto: @PeterObi
Asali: Twitter

Sai dai... nan fa daya inji NLC

Amma rahoton ya ce duk da ikirarin da Wabba ya yi, ‘yan kungiyoyin kwadago na NLC da ‘yan kasuwa na TUC sun ja baya da tafiyar Peter Obi.

Kusan za a iya cewa ba a ganin shugabannin kungiyoyin wajen yawon siyasa ko goyon bayan takarar Peter Obi da Yusuf Baba Ahmed a 2023.

A Satumban 2023, Wabba ya ce su na da mutanen da za su yi masu neman zabe a kowace karamar hukuma 774 da ake da ita a fadin kasar nan.

Kara karanta wannan

Fitaccen Dan Takarar Shugaban Kasa Yace Zai Ji Tsoron Allah Idan aka Zabe Shi a 2023

Shugaban ‘yan kwadagon ya ce akwai mutane miliyan 12 da a shirye suke su zabi ‘yan LP. Nan da kwanaki kusan 50 dai za a jarraba kafin su.

Shugaban Kasa ya tsira a majalisa

Bashin kudin da ke kan wuyan ‘Yan Najeriya Najeriya ya kai Naira tiriliyan 47, idan aka yi wasa adadin zai haura Naira Tiriliyan 70 zuwa bayan zabe.

An ji labari cewa ganin yawon aron kudin da ake yi ya fara yawa, wasu Sanatocin PDP da APC a Majalia sun dauki aniyar takawa Shugaban kasa burki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel