Dan Majalisar Kano Ya Yi Amai Ya Lashe, Ya Koma Jam'iyyar APC

Dan Majalisar Kano Ya Yi Amai Ya Lashe, Ya Koma Jam'iyyar APC

  • Dan majalisa mai wakiltar mazabar Gwale a majalisar dokokin Kano, Yusuf Babangida ya sake koma wa APC mai mulki
  • Babangida ya rubuta takardar murabus ranar 7 ga watan Janairu, 2023 ya aika wa shugaban NNPP na gundumar Sani Mainagge
  • Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan dan takarar shugaban kasa a inuwar APC ya gudanar da kamfe a jihar Kano

Kano - Mamba mai wakiltar mazabar Gwale a majalisar dokokin jihar Kano, Yusuf Babangida, ya sauya sheka daga NNPP mai kayan marmari zuwa APC mai mulki.

Jaridar Premium Times ta tattaro cewa Honorabul Babangida, makusanci ne kuma dan a mutun mai neman zama shugaban kasa a inuwar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso.

Sauya sheka a Kano.
Dan Majalisar Kano Ya Yi Amai Ya Lashe, Ya Koma Jam'iyyar APC Hoto: premiumtimesng
Asali: UGC

Dan majalisar ya tabbatar da ficewarsa daga NNPP ne a wata takarda mai dauke da kwanan watan 7 ga watan Janairu, wacce ya aika wa shugaban jam'iyar na gundumar Sani Mainagge, karamar hukumar Gwale.

Kara karanta wannan

Manyan 'Yan Takara 8 a Zaben 2023 Sun Jingine Tikitinsu, Sun Koma APC a Arewacin Najeriya

Ya ce ya yanke shawarin fita daga jam'iyar Kwankwaso ne saboda halin ko inkula da nuna wariya wanda ya hana NNPP zaman lafiya a cikin gida

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mista Babangida ya kara da cewa jam'iyar NNPP ta gurbata, 'Duk wata manufa ta demokaradiyya wanda ni kuma a kan tubalin da na gina siyasa ta kenan."

"Jam'iyar ta sanya son zuciya a gaba da komai, ga neman karfin iko kuma ba'a dauki walwala da maslahar masu ruwa da tsaki a bakin kamai ba."
Abubuwa dai sun bi sun cakude da sauran wasu dalilai da ban bayyana ba ne suka sa na ji bani da zabi illa na tattara na bar NNPP domin na samu damar tafiyar da siyasata a wani wurin."

Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ne ya karbi dan majalisar zuwa jam'iyya mai mulki a gidan gwamnatinsa da ke cikin birnin Kano.

Kara karanta wannan

Saraki Ya Nemi Gwamnan APC Ya Biya Shi Tarar N20b da Bashi Hakuri a Wata Kara Da Ya Shigar

Dikko Radda ya karbi masu sauya sheka daga PDP

A wani labarin kuma Dan Takarar Gwamnan Ya Takaita Atiku, Jiga-Jigai da Mambobin PDP Sun Koma Bayan Tinubu

Dan takarar gwamnan Katsina na APC, Dikko Radda, ya karbi daruruwam masu sauya sheka daga PDP a kananan hukumomi biyu.

Dakta Radda yayi alkawarin samar da ayyukan yi ga matasa, dawo da zaman lafiya, inganta lafiya da habaka Noma idan aka zabe shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel