Gwamnonin da Ake Rigima da su a PDP Sun Hadu a Ibadan, An Samu Labarin Matsayarsu

Gwamnonin da Ake Rigima da su a PDP Sun Hadu a Ibadan, An Samu Labarin Matsayarsu

  • Gwamnonin G5 da ke fada da Atiku Abubakar a PDP za su bayyana matsayarsu a garin Ibadan
  • Alamu na nuna cewa za iyi wahala duka Gwamnonin su karkata a kan goyon bayan ‘dan takara daya
  • Kowane Gwamna zai duba yadda siyasar Jiharsa ta ke tafiya a 2023 kafin ya iya goyon bayan wani

Oyo – Ana sa ran cewa Gwamnonin nan biyar da suka yi watsi da ‘dan takaran PDP a zaben shugabancin Najeriya, za su tsaida magana a yau Alhamis.

Tribune ta kawo rahoto a ranar 5 ga watan Junairu 2023 da ya yi nuni ga matsayar da Gwamnonin jihohin adawar za su dauka a kan zaben shugaban kasa.

Gwamnonin G5 watau Nyesom Wike, Samuel Ortom, Okezie Ikpeazu da Ifeanyi Ugwuanyi sun hadu a garin Ibadan tare da Gwamna Seyi Makinde.

Kara karanta wannan

2023: Hantar Tinubu, Atiku Da Obi Na Kaɗawa Yayin Da G5 Suka Dira Ibadan Don Sanar Da Wanda Za Su Marawa Baya

Kafin su fita yawon yakin neman zabe, Gwamnonin sun yi taro a daren ranar Laraba domin su karkare magana game da wanda za su marawa baya.

Duk wanda ya iya allonsa, ya wanke

A karshen zaman na jiya, jaridar ta ce ‘yan kungiyar na G5 sun fahimci ba za ta yiwu duk su hadu su goyi bayan ‘dan takara guda daga jam’iyya daya ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wadannan Gwamnoni sun fahimci cewa yanayin siyasar jihohisun sun bambanta da juna, don haka ba za su iya kakabawa dukkansu ‘dan takara guda ba.

'Yan APC
Yakin neman zaben APC Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

Majiya ta shaidawa cewa Gwamnonin Ribas da na Oyo watau Nyesom Wike da Seyi Makinde ba su gamsu cewa a goyi bayan takarar Peter Obi a LP ba.

Babu mamaki Gwamna Makinde yana ganin tallata ‘dan takaran na LP zai yi masa wuya a Oyo inda Bola Tinubu da jam'iyyar APC suke da karfi sosai.

Kara karanta wannan

2023: Tsohuwar Minista Ta Tsoma Baki, Ta Tona Asirin Mai Hana Ruwa Gudu a Rigingimun PDP

Bisa dukkan alamu, Gwamnan Benuwai watau Ortom, zai fadawa mutanen jiharsa su goyi bayan Peter Obi ne a maimakon Atiku Abubakar a zaben bana.

Wasu 'Yan G5 sun boye 'dan takaransu

Sauran gwamnonin da ke cikin tafiyar G5, Okezie Ikpeazu da Ifeanyi Ugwuanyi sun ki bayyana ‘dan takaran da suke goyon baya, sun bar abin a zuciyarsu.

A karshen zaman da za ayi a Ibadan, za a bukaci gwamnonin Abia da Enugu suyi wa ‘dan takaran da suke goyon baya aiki a asirce muddin ba Atiku ba ne.

Wata majiya ta ce gwamnonin ba za su fito karara su nuna inda suka sa gaba a zaben ba, misali zai yi wa gwamnan Enugu wahalar tallata Bola Tinubu.

Shin Tinubu bai da lafiya?

An ji labari Sakataren yada labaran Asiwaju Project Beyond 2023 kuma ‘dan kwamitin yakin zabe ya ce a daina damuwa da lafiyar Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

2023: Gwamnonin PDP Biyu Sun Ziyarci Abokin Gamin Atiku, Sun Fadi Abinda Suke Fatan A Yi Wa Su Wike G5

Adegboye Adebayo yana ganin aikin da Likitoci suka yi wa Tinubu a jikinsa ba zai hana shi yin mulkin Najeriya ba domin kwakwalwarsa garau ta ke.

Asali: Legit.ng

Online view pixel