Abin da ya sa Babu Ruwana da Yakin Neman Zaben Bola Tinubu Inji Ministan Buhari

Abin da ya sa Babu Ruwana da Yakin Neman Zaben Bola Tinubu Inji Ministan Buhari

  • Chris Ngige bai da wani ‘dan takaran da zai tallata a zaben shugaban kasa, ya ce kowanensu na shi ne
  • Ministan kwadagon ya kauracewa yakin neman zaben APC domin yana da alaka da duka ‘yan takaran
  • Ngige ya ce ya yi aiki da Atiku da Tinubu, kuma ya san Kwankwaso, sannan Obi ya gaje shi a Anambra

Abuja - Ministan kwadago da samar da ayyukan yi a Najeriya, Chris Ngige ya ce ya gujewa yakin neman zaben APC ne saboda duka ‘yan takaran sun cancanta.

Vanguard ta ce an ji Sanata Chris Ngige yana cewa mutane hudu da ke kan gaba wajen neman shugabancin kasa su na da kwarewar da za su iya rike Najeriya.

Ministan ya dura kan Olusegun Obasanjo wanda ya soki shugaba Muhammadu Buhari, Ngige ya yi kira ga mutane su zabi wanda ya yi tanadin taimaka masu.

Kara karanta wannan

Kaico: Tashin hankali yayin da mai siyar da fetur ya babbake abokinsa a kan cajar waya

Sanata Ngige ya yi magana ne a kauyensa na Alor a karamar Idemili ta Kudun jihar Anambra wajen rabon kayan kirismeti da gidauniyarsa tayi a cikin makon nan.

Ngige ya taimakawa marasa karfi

Da yake yi wa jama’a jawabi a cocin St. Mary a Alor, Ministan ya ce tun watan Satumban 2022, gwamnatin tarayya ta umarci su koma gida su taimaki mutane.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A game da wanda zai marawa baya a zaben shugaban kasa, Ngige ya ce dukkansu abokansa ne, sannan ya yi kira ga mutane su zabi wanda ke da manufofin kirki.

Minista
Tinubu, Ngige da Obi Hoto: gazettengr.com
Asali: UGC

“Abokai na ne kuma duk na san su. Sun yi aiki da ni ta hanya daya ko biyu kafin yanzu. Atiku Abubakar ya rike kasar nan lokacin da aka dauke ni ina Gwamna.
Tare da Asiwaju (Bola Ahmed Tinubu) muka kafa jam’iyyar Action Congress (AC). Tinubu aboki na ne kuma amini na a siyasa, ya taimaka mani da na ke Gwamna.

Kara karanta wannan

An Fallasa Sunan Dan Takarar Shugaban Kasan Da Tinubu Zai Amfani Da Shi Ya Lashe Zaben 2023

Mun yi aiki a ACN har na zama Sanatan adawa tilo a kaf Kudu maso gabas a ACN. Na san shi.
Peter Obi ‘danuwa na ne, karamar hukumarmu ta na kusa da ta shi, shi ne magaji na. Na san shi da kyau, na san irin kwarewarsa.
Rabiu Musa Kwankwaso na NNP aboki na ne shi ma. Na san shi da yana majalisa a lokacin Agunwa Anaekwe. Mun yi APC tare, saboda haka na san shi.

- Chris Ngige

Rahoton ya ce Ngige ya ce ba zai je yana yi wa wani ‘dan takara kamfe ba, kuma ba zai sauya-sheka ba, amma zai tabbatar ya yi abin da yake ganin ya dace.

An sauke Wazirin Bauchi

Dazu aka ji labari sabanin da aka samu tsakanin Gwamnan jihar Bauchi, Bala A. Mohammed da Atiku Abubakar ya shiga fadar Mai martaba Sarkin Bauchi.

Mai martaba Rilwanu Suleiman Adamu ya sauke Wazirinsa, Alhaji (Dr) Muhammadu Bello Kirfi saboda rashin girmama Mai girma Gwamna Bala A. Mohammed.

Kara karanta wannan

Babban Malamin Addini Ya Bayyana Wanda Zai Ci Zaben Shugaban Kasa Na 2023 A Najeriya

Asali: Legit.ng

Online view pixel