Babban Malamin Addini Ya Bayyana Wanda Zai Ci Zaben Shugaban Kasa Na 2023 A Najeriya

Babban Malamin Addini Ya Bayyana Wanda Zai Ci Zaben Shugaban Kasa Na 2023 A Najeriya

  • Wanda zai ci zaben shugaban kasa na 2023 zai zama wanda aka fi suka da kin jini cikin yan takarar
  • Wannan shine matsayin Prophet Joshua Iginla na cocin Champions Royal Assembly a yayin da ya ke bayyana abin da ya hango a 2023
  • Sai dai, ya ce dole yan Najeriya su yi addu'a ta yadda ba za a yi jinkirin sanar da sakamakon zaben ba

Prophet Joshua Iginla ya ce dan takarar da aka fi suka da kin jini ne zai ci zaben shugaban kasa na Najeriya a 2023.

Joshua Iginla, babban faston cocin Champions Royal Assembly a birnin tarayya Abuja, ya bayyana hakan ne yayin da ya ke bayyanawa mabiyansa da duniya abin da ya hango a 2023.

Iginla
Babban Malamin Addini Ya Bayyana Wanda Zai Ci Zaben Shugaban Kasa Na 2023 A Najeriya. Hoto: Joshua Iginla.
Asali: UGC

Ya ce:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Direktan Kamfen Din Matasa Na APC Ya Tafi Kan Dutse, Ya Yi Azumin Kwana 7 Da Addu'o'in Dare Don Nasarar Tinubu

"Ruhi na ta shiga cikin damuwa a watan Disamba sai Ruhi mai tsarki ya dauke ne zuwa wata balaguro. A siyasance, Ubangiji zai daukaka wani da ba kowa bane ya hadiye manyan.
"A shekarar 2023, wadanda ke bibiya na daga 2021, 2022 za su shaida cewa tun kadin zaben fidda gwani na jam'iyyu, Na ce Wike na da tasiri da shima Tinubu haka. Kuma za ku shaida abin da ya faru a 2022.
"Akwai bukatar mu yi addu'a don kada a samu jinkiri wurin sanar da sakamakon zabe. Ku fahimce ni, kada jam'iyya mai mulki ta saki jiki saboda na ga fada tsakanin zakuna biyu da damisa, musamman a zabukan gwamnonin jiha. Game da zaben shugaban kasa, na ga cewa dan takarar da aka fi kin jini da suka shine zai yi nasara da izinin Ubangiji."

Janar na kiristoci biyu za su mutu a wannan shekarar in ji babban malamin

Kara karanta wannan

Bidiyon Matar Aure Tana Gaggawar Ba Miji Abinci a Baki Kada ya Makara Aiki ya Janyo Cece-kuce

A wani rahoton daban, Prophet Joshua Iginla ya bayyana wa kiristoci cewa za a yi rashi a wannan shekarar.

Iginla, wanda shine shugaban cocin Champions Royal Assembly a Abuja a sakon da ya fitar na abubuwan da ya hango ya ce janar na kiristoci biyu za su mutu a 2023, Premium Times ta rahoto.

Da ya ke magana, malamin ya ce Ubangiji ne ya haska masa abubuwan da za su faru a shekarar mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel