Tinubu Ya Musanya Rade-Radin Fama da Cuta, Ya Fadi Abin da ke Nuna Koshin Lafiyarsa

Tinubu Ya Musanya Rade-Radin Fama da Cuta, Ya Fadi Abin da ke Nuna Koshin Lafiyarsa

  • Asiwaju Bola Tinubu ya karyata zargin da ake yi masa na cewa bai da isasshiyar lafiyar yin shugabanci
  • ‘Dan takaran shugaban kasar na Jam’iyyar APC ya ce masu wannan maganar karya suke yi masa
  • Tinubu ya ce bai dade da yin Umrah a Saudiyya ba, alhali ana rade-radin bai iya tafiya ko ya tsaya cak

Kano - ‘Dan takaran Jam’iyyar APC mai mulki, Asiwaju Bola Tinubu ya jaddada cewa garau take, bai fama da rashin lafiya kamar yadda ake ta rade-radi.

Asiwaju Bola Tinubu ya yi hira da gidan rediyon Freedom a ranar Litinin, bayan dawowarsa daga kasar Saudi Arabiya inda ya samu damar yin Umrah.

A jawabin da ‘dan takaran kujerar shugaban kasar ya fitar, ya bayyana ya zagaye dakin ka’aba sau bakwai a wajen dawafi yayin da yake birnin Makkah.

Kara karanta wannan

Tinubu Ko Atiku? Tsohon Gwamna Musulmi Ya Faɗi Wanda Allah Yace Zai Zama Shugaban Kasa a 2023

Tribune ta rahoto Bola Tinubu yana mai cewa haka ya yi Safa da Marwa kamar yadda addinin Musulunci ya yi tanadi, ba tare da wata gajiyawa ba.

Tsohon gwamnan na jihar Legas yake cewa mutum mara lafiya ba zai iya yin Umrah da kan shi ba.

“Ban dade da kammala Umrah ba. Nayi zagayen dawafi sau bakwai, kuma na hau Safa da Marwa sau bakwai duk ni kadai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ina mara lafiya zai iya yin wannan? Duk karya ce wannan ‘danuwa na.”
Tinubu
Bola Tinubu a jirgin sama Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

“Mutanen da suke wannan ikirari ba su da abin fada sai karyayaki da shirme. Na yi yawa, nayi magana a wurare, na tsaya na awanni na saurari mutane.
Da farko sun ce ba zan iya tafiya ba. Sun ce ba zan iya tsayawa cak ba, amma sun ji kunya.

Kara karanta wannan

2023: Abin da ya sa Mu ka Tsaida Bola Tinubu a Jam’iyyar APC Inji Sanatan Arewa

- Bola Tinubu

Jaridar nan ta Vanguard ta ce wannan ya zama martani ga masu cewa ‘dan takaran ba zai iya jagorantar ‘yan Najeriya ba, domin bai da cikakken lafiya.

Tinubu ya ce ya fi kowa shirin mulki

A cewar Tinubu, daga lokacin da aka fara kamfe zuwa yanzu, ya fi kowane ‘dan takara nuna cewa yana da dabarun da zai shawo kan matsalolin kasar.

“Ina da duk abin da ake bukata a zama shugaban tarayyar Najeriya, abin da nake roko a wajen mutanen kasar nan shi ne su duba ayyukan da nayi a da.
Ina so in yi wa kasar nan hidima, kun zan yi da kyau."

- Bola Tinubu

Wike ya yi wa Atiku habaici

A maimakon Obasanjo ya goyi bayan Atiku Abubakar ya zama shugaban kasa, an ji labari ya bada karfinsa ga Obi wanda ya fito ne daga Kudu maso gabas.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Dawo da Komai Baya, Ya Fadi Gaskiyar Batun Haduwarsa da Gwamnonin PDP

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya ce idan dai Mai gidan Atiku ba zai iya fadawa mutane su zabe shi ba, to shakka babu akwai katuwar matsala kenan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel