Fafutukar G5 Ta Wuce Babban Zaben 2023, Gwamnan Abiya Ya Yi Karin Haske

Fafutukar G5 Ta Wuce Babban Zaben 2023, Gwamnan Abiya Ya Yi Karin Haske

  • Gwamnan jihar Abiya yace tawagar tsagin Wike na kaokarin ganin an tabbatar da abinda zai amfani Najeriya har bayan 2023
  • Okezie Ikpeazu, mamba a tawagar G-5 bisa jagorancin gwamnan Ribas, yace duk abinda suke rigima a kansa na kan gaskiya
  • Har yanzun babu zaman lafiya a jam'iyyar PDP tun bayan gama zaben fidda ɗan takarar shugaban kasa a watan Mayu

Abia - Gwamnan jihar Abiya, Okezie Ikpeazu, yace fafukar ganin an tafi da kowa, daidaito da adalci da tawagar gwamnonin G-5 karkashin jagoranci Gwamna Nyesom Wike na Ribas ba iyakarsa zaɓen 2023 ba.

Gwamnan, ɗaya daga cikin mambobin G-5 da suka raba PDP biyu, yace fafutukarsu wani yunkuri ne na kara karfin adalci da daidaito a Najeriya.

Gwamnan Abiya.
Fafutukar G5 Ta Wuce Babban Zaben 2023, Gwamnan Abiya Ya Yi Karin Haske Hoto: vanguardngr
Asali: UGC

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa gwamna Ikpeazu ya yi wannan furucin ne yayin wata hira a Aba, babbar cibiyar kasuwanci ta jihar Abiya.

Kara karanta wannan

Bayan Raba Gari da Atiku, Gwamnonin G5 Sun Fara Kulla-Kullar Wanda Zasu Mara Wa Baya a 2023

A cewarsa, duk fafutukar da suke ba ta wuce batu kan a yi gaskiya, wanda a ganinsa ya yi karanci a fagen siyasar Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa, gwamnan ya ce:

"Akwai batu a kasa kuma batu ne na gaskiya, batun cika alƙawurran da aka ɗauka, batun wanda idan muka ce kai ne, to hakan ta kasance da zaran lokacin ya yi."
"Gaskiya zata saita kasar nan, ta samar da walwala ta yadda zamu yi maganin matsalolin tsaro, farfaɗo da tattalin arziki da sauran matsalolin da suka hana kasar mu motsa wa gaba."
"G-5 na magana ne kan abinda ya dace, ba iya 2023 kaɗai bane har gaba. Har a shekarar 2027 zan bukaci tsarin da zai jawo kowa ba tare da duba abinda sakamakon zaɓen 2023 ya kunsa ba."

Gwamnan ga kara da cewa burin tawagar G-5 a samu kwakkwarar arewa da take ganin girman kudu, kamar yadda suke fatan ganin Kudu na girmama arewa.

Kara karanta wannan

Bukola Saraki Ya Gargadi Hukumomin Tsaro Kan Batun Gwamnan CBN

PDP ta shiga matsala a jihar Filato

A wani labarin kuma Babban Jigon PDP Da Mambobin Jam'iyyar 20,000 Sun Sauya Sheka Zuwa APC a Jahar Filato

Babban jigon PDP a Filato kuma tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Umar Bantu, ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC

Mai magana da yawun APC a jihar Plateau, Mista Sylvanus Namang, ne ya sanar da ci gaban a ranar Lahadi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel