Sanatan PDP Mai Goyon Bayan Tinubu Ya Gana da Kwamitin Yakin Neman Zaben APC

Sanatan PDP Mai Goyon Bayan Tinubu Ya Gana da Kwamitin Yakin Neman Zaben APC

  • Sanata Chimaroke Nnamani ya hadu da wasu daga cikin ‘yan kwamitin yakin neman zaben APC a 2023
  • Tsohon gwamnan na jihar Enugu ya na sa ran Bola Tinubu zai lashe zabe, duk da yana jam’iyyar PDP
  • Chimaroke Nnamani ya ce babu abin da ya hada goyon bayan APC da yake yi da kwadayin abin Duniya

Enugu - Tsohon gwamnan jihar Enugu, Chimaroke Nnamani ya sake jaddada goyon bayan shi ga Asiwaju Bola Tinubu mai neman shugabancin Najeriya.

Sanata Chimaroke Nnamani mai wakiltar Enugu ta gabas a majalisar dattawa ya ce Bola Tinubu za a zaba a shekarar badi, The Nation ta kawo rahoton.

‘Yan kwamitin yakin neman zaben Bola Tinubu, suka fitar da matsayar ‘dan siyasar a lokacin da suka ziyarci gidansa a Agbani a garin Nkau a jihar Enugu.

Kara karanta wannan

Magoya Bayan Jonathan Sun Tsaida ‘Dan Takara, Sun Shiga Yi wa Tinubu Kamfe a Kudu

‘Yan kwamitin APC da suka gana da tsohon Gwamnan sun hada da tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Ken Nnamani da Onyemuche Nnamani.

A tawagar akwai Kakakin PCC na Kudu maso gabas, Onyemuche Nnamani da A. C. Udeh.

Sanata Nnamani ya fadawa ‘yan tawagar cewa ba saboda neman abin Duniya yake goyon bayan Tinubu ba, sai saboda abin da Ibo za su samu a siyasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Chimaroke Nnamani
'Yan APC tare da Sanata Chimaroke Nnamani Hoto: www.vanguardngr.com
Asali: UGC
"A ranar 25 ga watan Fubrairu 2023, za a zabi Asiwaju Bola Tinubu a matsayin sabon shugaban kasar Najeriya.
Ya kamata mutane su fahimci zabi na (Tinubu) ba saboda abin Duniya ba ne, sai saboda a shigo da Ibo siyasa."

- Sanata Chimaroke Nnamani

APC PCC ta yabi Nnamani

Vanguard ta rahoto Josef Onoh yana yabon tsohon Gwamnan kan yadda ya jajirce a kan takarar Bola Tinubu, ya ce saboda gobe tayi kyau yake neman mulki.

Kara karanta wannan

Gwamnonin da Suka Yi Wa Atiku Bore Sun Karkata a Kan ‘Yan Takara 2 a Zaben 2023

Kwamitin yakin zaben ya jinjinawa Nnamani ganin yadda ya jajirce da yarjejeniyar da aka yi a Asaba, Enugu da Legas a kan maida mulki zuwa yankin Kudu.

“Na godewa Chimaroke Nnamani da ya tsaya tsayin-daka wajen ganin Asiwaju ya zama shugaban kasar Najeriya.
Asiwaju a matsayinsa na uban kowa ya ce ya zo ne domin yana da kokarin da zai tabuka a ko ina kasar, kuma shakka babu ina tare da Asiwaju."

- Josef Onoh

Atiku ko Tinubu?

An ji labari ‘Dan takaran Shugaban kasa a NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso ya ce abokan gwabzawarsa sun gaji, ba za su iya mulkin Najeriya ba.

Rabiu Kwankwaso ya ce ya fi abokan gabansa ilmin boko domin yana da PhD.

Asali: Legit.ng

Online view pixel