Gwamna Inuwa Yahaya Ya Fallasa Asirin Yan Siyasan Da Basu Son Amfani da BVAS a 2023

Gwamna Inuwa Yahaya Ya Fallasa Asirin Yan Siyasan Da Basu Son Amfani da BVAS a 2023

  • Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya ya ce ko kaɗan ba ya jin tsoron amfani da na'urar BVAS wajen tantance masu kaɗa kuri'a a 2023
  • Gwamnan, wanda ke neman ta zarce a kujerasa yace yan siyasan da basu taɓuka wa talakawa komai ba ke tsoron fasahar zamanin
  • Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC ta fara rabon na'urar a sassan jihar Gombe gabanin 2023

Gombe - Gwamnan jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, ya ce ba ya tsoron matakin hukumar zabe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) na amfani da na'urar tantancewa BVAS a zaben 2023.

A cewar gwamna Yahaya, 'yan siyasan da basu da magoya baya ne kaɗai suke jin tsoron sabon tsarin da hukumar zaben ta zo da shi, kamar yadda jaridar Punch ta rahoto.

Muhammad Inuwa Yahaya.
Gwamna Inuwa Yahaya Ya Fallasa Asirin Yan Siyasan Da Basu Son Amfani da BVAS a 2023 Hoto: Inuwa Yahaya
Asali: Facebook

Gwamnan ya yi wannan furucin ne yayin gangamin kamfe ɗinsa wanda ya gudanar Garko, inda ya jaddada cewa talakawa na tare da shi har gobe.

Kara karanta wannan

Bayan Raba Gari da Atiku, Gwamnonin PDP 5 Zasu Gana da Ɗan Takarar da Suke Shirin Goyon Baya a 2023

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa zuwa yanzun hukumar INEC ta raba na'urorin BVAS aƙalla 2988 gabanin babban zaɓen 2023.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Bayanai sun nuna cewa tun da farko gwamna Yahaya ya ziyarci yankunan Gona, Amada, inda ya nemi goyon bayan Lamidon Gona, Abdulkadiri Abdulsalam, game da kokarinsa na tazarce.

"Idan har da BVAS, 'yan siyasan da ba su da masoya ne kaɗai zasu firgita da zaɓe," inji gwamna Yahaya.

Gwamnan ya bayyana cewa kafin zuwan wannan saabuwar na'urar, Card Reader tana taimakawa 'yan siyasa wajen magudin zaɓe. A cewarsa duk wanda ya yi wa talakawa abin alheri zai gani a Akwatun zaɓe.

"A baya 'yan siyasa na iya murɗe zabe amma zuwan BVAS ya nuna idan baka da magoya baya ba zaka kai labari ba saboda ba zaka iya magudi ba kamar Card Reader."

Kara karanta wannan

Atiku Ya Sake Shiga Tasku, Gwamna Arewa Ya Ayyana Ɗan Takarar Da Zai Marawa Baya a 2023

Legit.ng Hausa ta rahoto cewa gwamna Yahaya ya ziyarci gundumomi uku a ci gaba da yakin neman tazarcensa a kujerar gwamnan Gombe a zaɓe mai zuwa.

Zan Sanar da Ɗan Takarar Shugaban Kasan Da Zan Wa Aiki a Janairu, Wike

A wani labarin kuma Gwamnan jihar Ribas ya sha alwashin sanar da Yan Najeriya ɗan takarar da zai wa kamfe bayan raba gari da Atiku

Idan baku manta ba, Wike da wasu gwamnoni PDP da ake kira G5 sun tsaya tsayin daka kan bukatar cewa wajibi shugaban PDP na ƙasa ya yi murabus.

A halin yanzun dai duk wata tattauna wa da ake don shawo kan fusatattun gwamnonin ta wargaje, sun fara shirn kayar da Atiku a 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel