Kiristoci Sun Gudanar Da Addu’o’i Na Musamman Domin Nasarar Tinubu A Zaben 2023

Kiristoci Sun Gudanar Da Addu’o’i Na Musamman Domin Nasarar Tinubu A Zaben 2023

  • Kiristoci a jihar Oyo sun yi wa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu addu'a na musamman don nasara a zaben 2023
  • Wani basaraken Oyo ya ce bai kamata ayi la'akari da addini ba a zabe don ci gaban Najeriya
  • Shugabanni da kungiyoyin musulunci ma sun gudanar da nasu addu'o'in na goyon bayan takarar Tinubu

Oyo - Mabiya addinin Kirista a jihar Oyo sun taru a karshen mako tare da yiwa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu addu'an samun nasara a zaben 2023.

Taron wanda ya samu halartan wakilan kungiyoyin kiristoci kimanin su 1,000, ya gudana ne a otel din Ilaji da ke Akanran, Ibadan, babban birnin jihar Oyo, jaridar The Nation ta rahoto.

Bola Tinubu
Kiristoci Sun Gudanar Da Addu’o’I Na Musamman Domin Nasarar Tinubu A Zaben 2023 Hoto: @OfficialABAT
Asali: Twitter

Wadanda suka halarci taron sun hada da shugaban kungiyar kiristocin Najeriya reshen Ibadan, mataimakin shugaban kungiyar CAN, shugabannin CAN a Lagelu, Ido, Ibadan ta kudu maso yamma, Ibadan ta arewa,.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Tinubu, Ganduje, El-Rufai na can a Kaduna don kaddamar da kamfen APC a Arewa maso Yama

Har ila yau, shugabannin CAN na Ibadan ta arewa maso yamma, Egbeda, Akinyele, Oluyole, Ibadan ta kudu maso gabas da mataimakin ciyaman na karamar hukumar Ona Ara sun hallara.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kada a duba addini wajen zaben shugaba nagari

Da yake jawabi a taron, wani babban basaraken Ibadan, Dotun Sanusi wanda ya samu wakilcin Mogaji Nurudeen Akinade, ya ce dole a duba sama da addini don Najeriya ta ci gaba.

Ya ce Asiwaju Tinubu shine mafita ga matsalar da kasar ke fuskanta a yanzu.

Kungiyoyin Musulmai sun yiwa Tinubu addu'a a Oyo

A wani labari makamancin wannan, shugabanni da kungiyoyin Musulunci daga fadin jihar Oyo sun ayyana goyon bayansu ga Bola Tinubu ta hanyar yi masa addu'a, rahoton independent.

Taron ya gudana ne a yankom Ona Ara da ke garin Ibadan.

Cif Dotun Sanusi, mamallakin otel din Ilaji and Sports Resort ne ya dauki nauyin taron don ayyana goyon baya ga Tinubu.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Tinubu Ya Dira Kaduna Don Taron Yakin Neman Zabe Ranar Talata

Sanusi ya ci gaba da tara kunhiyoyi da shugabannin manyan kungiyoyi na mazauna Ibadan, don goyon bayan babban dan takarar shugaban kasar.

Shahararren malamin Musulunci, Sheikh Hamad alAlfulanny ne ya jagoranci taron.

Ya kuma samu halartan Sheikh Abdulganiy Abubakry, babban limamin Ibadan da sauran manyan limamai daga yankunan jihar baki daya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel