An Jibgi Jigon PDP Kan Sanya Rigar Atiku Wajen Kamfen Din Gwamna Ortom a Jihar Benue, Bidiyo Ya Bayyana

An Jibgi Jigon PDP Kan Sanya Rigar Atiku Wajen Kamfen Din Gwamna Ortom a Jihar Benue, Bidiyo Ya Bayyana

  • An yiwa wani jigon PDP a jihar Benue dukan kawo gishiri a wajen gangamin yakin neman zaben Gwamna Samuel Ortom a yankin Gboko
  • Tsohon shugaban karamar hukumar Ushongu, Asawa Joe, ya ci na jaki saboda ya halarci gangamin sanye da riga mai hoton Atiku Abubakar
  • Joe ya ce ya shiga dimuwa domin sai a kan gadon asibiti ya samu ya farfado

Benue - Asawa Joe, tsohon shugaban karamar hukumar Ushongu da ke jihar Benue, ya ce an ci zarafinsa a wajen gangamin yakin neman zaben Gwamna Samuel Ortom wanda aka yi a ranar Talata saboda ya sanya rifar Atiku.

Jigon na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya bayyana hakan ne a cikin wani bidiyo da Vershima Aondoakaa ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Talata.

Kara karanta wannan

Jami'iyar APC Nakasu Kawai Ta Kawo A Nigeria Tsawon Lokacin da ta Shafe Tana Mulki, Atiku

Jigon PDP
An Jibgi Jigon PDP Kan Sanya Rigar Atiku Wajen Kamfen Din Gwamna Ortom a Jihar Benue, Bidiyo Ya Bayyana Hoto: Asawa Joe, Vershima Aondoakaa
Asali: Facebook

Asawa, wanda ya ce shi mamba ne na kungiyar 'Atiku Grassroot Movement' a jihar Benue, ya ce ya yanke shawarar zuwa wajen ne a lokacin da ya samu labarin cewa Gwamnna Ortom zai kaddamar da yakin neman zabensa a Gboko.

Mutum fiye da 50 ne suka far mun da naushi: Asawa Joe ya yi bayanin halin da ya tsinci kansa a ciki

Jigon na PDP ya yi bayanin halin da ya shiga a wajen gangamin yakin neman zaben Ortom:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"An yi mun dukan da ban taba shan irinsa ba a rayuwana a wajen gangamin kamfen din PDP na yanki, kuma ba a sanmu da rikici ba a wajen kaddamar da kamfen din gwamnanmu na neman kujerar sanata. Wato mun samu labarin cewa gwamnan zai kaddamar yakin neman zabensa a Gboko a yau.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Dan takarar gwamnan APC ya ce zai yi amfani da baiwar 'Yahoo Boys'

"Ni mamba ne a kungiyar 'Atiku Grassroot Movement' a jihar Benue, kuma da muka samu labarin nan, sai muka ga cewa wannan aiki ne na PDP kuma dama ce garemu mu je sannan mu nuna karfin PDP a Gboko. Don haka muka tara mambobinmu saboda mun samu labarin cewa kungiyoyin PDP daban-daban za su kasance a wajen, sannan muka wayar da kan mutanenmu, muka kawo su nan. Don haka muka shiga ciki.
"Da na zo nan, na shiga ciki sannan na je na yi musabaha da mutanen kujerar manyan baki saboda ni ne tsohon shugaban karamar hukumar Ushongu da ya sauka kuma ina cikin harkokin PDP dumu-dumu kuma an fada masa cewa a Benue, PDP daga kasa ne zuwa sama kuma wannan shine sakon da shugabanmu na PDP na kasa ke ta isarwa kuma kwatsam sai muka zo nan tare da nufin cewa za mu saka PDP alfahari. Da muka zo nan bamu sani ba kuma ban ma lura cewa akwai alamu na sauyin sako da dabi'a.'

Kara karanta wannan

Shugaban Kasa a 2023: Idan Na Hau Kujerar Mulki Matasa Za Su Sha Romon Dadi, Atiku Abubakar

"Wadanda suka tunkara ni sun tambayeni cewa wa ya aiko ni nan kuma wa ya ce na saka wannan rigar? Wannan ne rigar da suka jibge ni da ita sannan suka yaga ta suka jefar, kuma suka ce ban samu umurnin cewa basa son ganin kowani abu mai kama da PDP ba a na. Wannan shine abun da na ji daga wajensu, sai suka far mun, suna ta duka na da karafuna, kafafunsu, hannayensu, suna naushina ta hagu da dama.
"Mutum fiye da 50 ne suka dunga jibgata, wani shugaban matasa a nan Gboko, Shawa Uge, ne ya ceci rayuwata."

A wata wallafa da Joe ya yi a shafinsa na Facebook, ya ce an masa duka har sai da ya shide sannan ya farfado a gadon asibiti.

Ya ce:

"Nagode Allah! Yanzu na farfado a asibiti. An yi mun duka har sai da na shide kan na saka rigar Atiku a gangamin PDP a Gboko."

Kara karanta wannan

Ya’yan Buhari sun shiga yakin neman zaben mata na Tinubu-Shetima a Katsina

Jama'a sun yi martani

Bishop Joe Ichull ya ce:

"Asawa Joe. Wannan babban kasada ne. Ka kiyaye a gaba ka fahimci ta inda iska ke kadawa kafin tashi jirginka."

Martins Bagidi ya ce:

"Ka je neman magana ne ai idan basa yin Atiku menene dalilinka na yawo da rigar Atiku a jikinka a wajen taronsu?"

Anda Orhirga Anda ya ce:

"Ciyaman! Kai kadai ne mutumin da ke sanye da rigar Atiku? Menene dalilin da yasa labarinka ya sha banban?"

Zaban Atiku Abubakar a 2023 daidai yake da zaban Bayarabe, Titi

A wani labarin, Titi Atiku Abubakar ta roki al'ummar yankin kudu maso yammacin Najeriya a kan su zabi mijinta domin ya zama shugaban kasa a 2023.

A cewar Titi, ta haka ne za a samu bayarabiya ta farko da zata rike matsayin matar shugaban kasar Najeriya a tarihin kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel