Dan Takarar Gwamnan APC Yayi Alkawarin Yin Amfani da Baiwar da Allah Ya Yiwa ‘Yahoo Boys’

Dan Takarar Gwamnan APC Yayi Alkawarin Yin Amfani da Baiwar da Allah Ya Yiwa ‘Yahoo Boys’

  • Dan takarar gwamna a jam'iyyar APC ya bayyana yadda zai yi amfani da matasa 'yan damfara wajen ciyar da jiharsa gaba
  • Mataimakin shugaban majalisar dattawa ya ce, gwamnatin Okowa ta runtumo bashin da zai illata jihar da yake neman gwamna
  • A bangare guda, ya ce zai yi ayyukan tituna da suka lalace a jihar tare da neman gwamnatin tarayya ta mayar masa da kudaden

Jihar Delta - Mataimakin shugaban majalisar dattawa kuma dan takarar gwamna a jam'iyyar APC a jihar Delta, Ovie Omo-Agege ya yi alkawarin yin amfani da baiwar da Allah ya yiwa 'Yahoo Boys'; matasa 'yan damfara ta yanar gizo ta hanyar da ta dace.

Dan takarar ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a yayin kamfen dinsa a karamar hukumar Aniocha ta Arewa a jihar gabanin zaben 2023.

Kara karanta wannan

Ya’yan Buhari sun shiga yakin neman zaben mata na Tinubu-Shetima a Katsina

Yankin da gwamnan ya yi gangaminsa na kamfen ya kunshi al'ummomin Onicha-Ugbo, Issele-Uku, da Onicha-Olona, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Dan takarar gwamnan APC ya ce zai jawo 'yan damfara kusa dashi saboda tsaro
Dan Takarar Gwamnan APC Yayi Alkawarin Yin Amfani da Baiwar da Allah Ya Yiwa ‘Yahoo Boys’ | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Dan takarar APC ya caccaki PDP, ya bayyana yadda zai yi amfani da 'Yahoo Boys'

A cewarsa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Gwamnatin jihar Delta a karkashin Okowa ta karbi N2.8tr da wasu N340bn daga shugaba Buhari kuma duk da haka ta ci bashin N400bn ba tare da yin wani aikin a zo a gani ba da zai nuna an kashe kudaden da jihar ta karba.
"A yau, gaba dayan mutanen Delta, har ma da yaran da ba a haifa ba, ana binsu bashin da Okowa ya runtumo.
"Saboda haka, mu jama'ar Delta mun yanke kuma mun amince Okowa ba zai yi wa'adi na uku ba ta hanyar amfani da Sheriff Oborevwori."

A bangare guda, dan takarar ya ce zai samar da ayyukan yi halastattu ga 'yan damfarar yanar gizo, inda zai zuba jari ga dukkan mahajojin da suka kirkiri, The Informant ta tattaro.

Kara karanta wannan

Gwamnan Babban Jihar Arewa Ya Faɗa Wa Ƴan Najeriya Wanda Ya Cancanta Su Zaɓa Shugaban Kasa A 2023

"Za mu yi amfani da baiwa da kwarewar Yahoo Boys ta daura su a kan turbar da suka fi kwarewa akai amma ta halastacciyar hanya, za mu umartarce su da su kirkiri manhajoji, gwamnati kuma za ta sa hannun jari. Ta yin haka, za mu kirkiri ayyuka ga 'ya'yanmu.
"Za mu yi ayyukan titunan gwamnatin tarayya da suka lalace sannan mu nemi a mayar mana da kudin saboda jama'ar Delta ne ke amfani da hanyoyin."

A makon nanne jam'iyyar APC za ta gudanar da taron gangamin kamfen dinta a jihar Bayelsa, duk dai a Kudancin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel