Duk Wanda Ke Da Shakku Kan Shekarun Tinubu Ya Tafi Wurin Marigayiyar Mahaifiyarsa Ya Tambaye Ta, Gbajabiamila

Duk Wanda Ke Da Shakku Kan Shekarun Tinubu Ya Tafi Wurin Marigayiyar Mahaifiyarsa Ya Tambaye Ta, Gbajabiamila

  • Femi Gbajabiamila, kakakin majalisar dokokin tarayyar Najeriya ya bada amsa ga yan Najeriya da ke shakku kan shekarun Bola Tinubu
  • Gbajbiamila ya ce dukkan wadanda ke shakku kan da shekarun dan takarar shugaban kasar na APC su tafi su tambayi mahaifiyarsa
  • Alhaja Abibatu Mogaji, Iyaloja Janar na Najeriya, mahaifiyar tsohon gwamnan na jihar Legas ta rasu a watan Yunin shekarar 2013

Jihar Legas - Kakakin majalisar dokokin tarayyar Najeriya, Femi Gbajabiamila ya soki wadana ke tambayoyi game da shekarun dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu, Channels TV ta rahoto.

Duk da cewa bayanai da ke kafafe sun ce shekarun Tinubu 70 ne, yan Najeriya da dama suna ikirarin ya fi hakan tsufa.

Femi daTinubu
Duk Wanda Ke Da Shakku Kan Shekarun Tinubu Ya Tafi Wurin Marigayiyar Mahaifiyarsa Ya Tambayeta, Gbajabiamila. Hoto: @SaharaReporters.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Jihar Kano Da Wasu Jihohin Arewa 5 Da Nike Da Tabbacin Zan Lashe: Tinubu

Gbajabiamila ya kare dan takarar na APC ne yayin takaitaccen jawabin da ya yi wa manema labarai yayin kamfe din takarar shugaban kasa da gwamna a Legas.

Gbajabiamila: Duk mai shakku kan shekarun Tinubu ya tafi wurin mahaifiyarsa ya tabbatar

Gbajabiamila ya bayyana Tinubu a matsayin dan siyasa mafi kasaita a zamanin yanzu a Najeriya.

Ya ce:

"Za su tambaye ku shekarunsa. Ku fada musu shekarunsa daidai da abin da mahaifiyarsa ta ce. Idan kuma suna da shakku ku fada musu su tafi wurin mahaiyarsa su tabbatar.
"Idan sun ce bai yi karatu ba. Ku fada musu idan an gwamutsa dukkan yan takarar wuri guda, ya fi su ilimi. Idan sun ce muku ana nemansa ruwa a jallo a Amurka. America ta nanata cewa ba su san abin da suke fada ba.
"Idan sun ce ya aikata rashawa, fada musu cewa shine wanda aka fi bincika a tarihin Najeriya kuma ba a same shi da laifi ba."

Kara karanta wannan

Saboda Tsabagen Girmamawa, An Sanyawa Titi Sunan Muhammadu Buhari a Kasar Waje

Mahaifiyar Tinubu, Alhaja Abibatu Mogaji, wacce ita ce Iyoloja Janar na Najeriya ta rasu a watan Yunin 2013.

Akwai wani rubutu a kafafen intanet da marigayi Yinka Odumakin, tsohon kakakin Afenifere ya yi, inda ya yi ikirarin cewa tsohon gwamnan na Legas ya dara shekaru 70, Sahara Reporters ta rahoto.

A shekarar 2018, Odumakin ya yi rubutu kunshi uku da ya yi wa take "hoton damisan da Ambode ya yi sukuwa a kai" ina ya bayyana abin da ya sani game da Tinubu.

Abin da aka tattaunawa tsakanin Janar Ibrahim Babangida da Tinubu da suka hadu

Asiwaju Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, a ranar 8 ga watan Nuwamban 2022 ya gana da Ibrahim Babangida.

Tsohon gwamnan na jihar Legas ya ziyarci tsohon shugaban kasan na mulkin soja a gidansa da ke Minna, Neja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel