An Samu Labarin Abin da Janar Ibrahim Babangida Ya Bijirowa Tinubu da Aka Hadu

An Samu Labarin Abin da Janar Ibrahim Babangida Ya Bijirowa Tinubu da Aka Hadu

  • Asiwaju Bola Tinubu ya kai ziyara ta musamman wajen Janar Ibrahim Badamasi Babangida mai ritaya
  • Ibrahim Badamasi Babangida ya tambayi Tinubu ko mutane na ba shi isasshiyar damar da zai rika hutawa
  • ‘Dan takaran shugaban kasar ya shaidawa tsohon shugaban kasar da karfi da yaji yake samun lokacin hutu

Minna - A ranar Talata, 8 ga watan Nuwamba 2022, Asiwaju Bola Tinubu mai neman zama shugaban Najeriya, ya zauna da Ibrahim Badamasi Babangida.

‘Dan takaran shugaban kasar na jam’iyyar APC mai mulki ya kai ziyara zuwa gidan Janar Ibrahim Badamasi Babangida da ke kan dutse a Minna, jihar Neja.

A wajen tattaunawarsu, Legit.ng ta samu labari Janar Ibrahim Babangida ya tambayi ‘dan takaran ko ‘yan tawagarsa su na kyale shi ya samu damar hutawa.

Ganin shekarunsa sun yin isa da irin wahalar yakin neman zaben shugaban kasa a Najeriya, akwai bukatar Tinubu ya yi a hankali domin ya kula da lafiyarsa.

Kamar yadda aka ji daga wani bidiyo da aka wallafa a Twitter, Babangida ya fahimci duk wadanda ke cikin tawagar ‘dan takaran matasa ne masu jini a jika.

Da ya ke ba tsohon shugaban Najeriyan amsa, Tinubu yace yana ba jikinsa hutu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Babangida da Tinubu
Ibrahim Babangida da Bola Tinubu Hoto: @FS Yusuf
Asali: Twitter

Babangida ya ce masa:

“Ka na lafiya?
Su na kyale ka huta kuwa?

Sai Tinubu yace:

“Su na yi (ba ni damar hutawa)
Kuma ni ma ina tursasawa kai na….”

Babangida ya cigaba:

“Dukkansu masu kananan shekaru ne.”

Shi kuwa Tinubu yace:

“Eh”.

Kwanakin baya Rabiu Kwankwaso mai neman takarar shugaban kasa a NNPP ya yi kira ga Bola Tinubu ya bi yakin neman takara a hankali, ya kula da lafiyarsa.

Amma Femi Fani Kayode wanda darekta ne a kwamitin takarar APC a zaben shugaban kasa, yace ‘dan takaransu ya fi duka abokan karawarsa koshin lafiya.

Mogaji, Obas, YCE sun bi Bola Tinubu

A baya rahoto ya zo cewa wasu Dattawan kasar Yarbawa sun tabbatar da goyon bayansu ga Asiwaju Bola Tinubu a zaben shugaban kasar da za ayi a badi.

Manyan Yarbawa sun yi kira na musamman ga ‘yan kabilarsu su zabi Tinubu. SWAGA ta na so 'dan takaransu ya samu kuri'a miliyan 15 daga yankinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel