Zaben 2023: PRP Ta 'Rushe' A Sokoto, Dukkan Yan Takarar Ta Sun Koma APC

Zaben 2023: PRP Ta 'Rushe' A Sokoto, Dukkan Yan Takarar Ta Sun Koma APC

  • Babban jam'iyyar hamayya a jihar Sokoto, APC, ta samu tagomashi a yayin da daukakin yan PRP suka dawo cikinta
  • Sai'idu Muhammad Gumbarawa, dan takarar gwamna na PRP, wanda ya yi wa sauran yan takarar jagora ya ce sun shigo APC ne don bada gudunmawarsu ga cigaban jihar
  • Wamakko, jigon APC a Sokoto, ya bayyana farin cikinsa tare da yi wa dukkan yan PRP da suka shigo APC adalci

Jihar Sokoto - Yan watanni gabanin babban zaben 2023, baki daya yan jam'iyyar Peoples Redemption Party, PRP, sun koma jam'iyyar All Progressives Congress a jihar, rahoton The Punch.

Gaba daya shugabannin jam'iyyar karkashin dan takarar gwamnan ta, Sa'idu Muhammad Gumburawa, sun fita daga jam'iyyar zuwa APC.

PRP and APC
Zaben 2023: PRP Ta 'Rushe' A Sokoto, Dukkan Yan Takarar Ta Sun Koma APC. Hoto: @MobilePunch.
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Da Gaske Jam'iyyar PRP Ta Rushe Cikin APC a Sakkwato? An Fayyace Gaskiyar Lamari

Wadanda suka sauya shekan sun hada da yan takarar sanatoci uku a jihar, dukkan yan takarar majalisar wakilai na tarayya, yan takarar majalisar jiha da shugabanninta na jiha zuwa kananan hukumomi.

Jagoran jam'iyyar, wanda kuma shine dan takarar gwamna a jihar, Saidu Muhammad Gumburawa ya sanar da jagoran APC, Sanata Aliyu Wamakko cewa sun yanke shawarar barin tsohuwar jam'iyyarsu ne don cigaba da bada gudunmawarsu wurin ganin nasarar APC a jihar a zaben 2023 da ke tafe.

Ya kara bayanin cewa duba da halin da jihar ta tsinci kanta a ciki karkashin gwamnatin PDP, sun taho APC su hada gwiwa da shugabanninta don cin zabe don jihar ta koma yadda ta ke a baya karkashin gwamnatin tsohon gwamna, Aliyu Wamakko.

Wamakko ya yi maraba da wadanda suka shio APCn

A jawabinsa, Wamakko ya yi maraba da sabbin mambobin ya kuma bayyana Gumburawa a matsayin aboki sannan abokin huldar cigaba.

Kara karanta wannan

'Dan Takarar Gwamna, 'Yan Takarar Majalisar Tarayya da Majalisar Jiha Sun Aje Tikitinsu, Sun Koma APC a Jihar Arewa

Kamar yadda Within Nigeria ta rahoto, tsohon gwamnan na Sokoto ya bayyana farin cikinsa da shigowarsu APC kuma ya bayyana APC a matsayin jam'iyyar wadanda ke son ganin cigaban Sokoto.

Ya bawa Gumburawa tabbacin APC za ta yi aiki da shi da magoya bayansa kut-da-kut don tabbatar da aiki cikin zaman lafiya a koda yaushe.

Hadimin Tambuwal Da Jigon PDP A Sokoto Sun Sauya Sheka Zuwa APC

Mashawarci na musamman ga Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na Sokoto, Bello Malami, ya bar jam'iyyar PDP ya koma APC a yayin da ake tunkarar zaben 2023.

Kazalika, jigon jam'iyyar PDP mai mulki a Sokoto, Alhaji Umaru Chori Sanyima shima ya fita daga jam'iyyar ta PDP ya sauya sheka zuwa APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel