2023: Dan Takarar Gwamna da Masu Neman Majalisa Sun Aje Tikiti, Sun Koma APC

2023: Dan Takarar Gwamna da Masu Neman Majalisa Sun Aje Tikiti, Sun Koma APC

  • Baki ɗaya 'yan takarar jam'iyyar PRP a jihar Sokoto sun aje tikitinsu, sun koma jam'iyyar APC a jihar Sokoto
  • Ɗan takarar gwamna, Sa'idu Gumburawa, ne ya jagoranci yan takarar majalisun tarayya na majalisar dokokin jiha zuwa APC
  • Sanata Aliyu Wamakko, wanda ya tarbi masu sauya sheƙar hannu biyu, yace wannan ba ƙaramar nasara bace

Sokoto - 'Yan takarar kujeru daban-daban na jam'iyyar PRP a jihar Sakkwato karkashin jagorancin ɗan takarar gwamna a 2023, Sa'idu Gumburawa, sun sauya sheƙa zuwa APC.

A cewar hukumar labarai ta ƙasa (NAN), hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da Bashar Abubakar, mai magana da yawun tsohon gwamnan jihar, Sanata Aliyu Wamakko, ya fitar.

Tutar jam'iyyar PRP.
2023: Dan Takarar Gwamna da Masu Neman Majalisa Sun Aje Tikiti, Sun Koma APC Hoto: thecableng
Asali: UGC

Da yake jawabi kan matakin da suka ɗauka, Gumburawa yace 'yan takarar PRP sun shiga APC ne domin ba da gudummuwarsu wajen tabbatar da nasarar jam'iyyar a zaɓen 2023.

Kara karanta wannan

2023: APC Ta Hargitse a Jihar Arewa Yayin da Wani Sanatan Jam'iyyar Ya Gana da Ɗan Takarar PDP

Ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Mun yi nazari kan halin da Sakkwatawa suka shiga karkashin mulkin PDP kuma hakan ya ƙara man kwarin guiwar shiga APC domin taimaka wa jiharmu ta dawo kan turbar nasara da take a mulkin Wamakko."

Bayan Gumburawa, sauran waɗanda suka bi sawunsa zuwa APC sun hada da 'yan takarar Sanata na shiyyoyi uku a inuwar PRP, Garzali Abdullahi, Bello Holai da Shehu Ibrahim.

"Haka nan kuma 'yan takarar majalisar wakilan tarayya 11 da masu neman shiga zauren majalisar dokokin jihar Sokoto 30 na cikin waɗanda suka koma APC," inji Abubakar, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Wannan babbar nasara ce a APC - Wamakko

Sanarwan ta ƙara da cewa 'yan takarar jam'iyar PRP a 2023 sun samu tarba hannu bibbiyu daga jagoran jam'iyyar APC a Sakkwato, Sanata Wamakko.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Surukin Shugaba Buhari Ya Sauya Sheka Daga APC, Ya Fadi Dalili

Da yake jawabi kan cigaban, Wamakko yace wannan sauya sheƙar na ɗaya daga cikin manyan nasarorin da APC ta samu a jihar gabanin babban zaɓen 2023.

"Na ji daɗi abokina kuma abokin kokarin kawo cigaba, Gomburawa, ya dawo gida ya haɗa hanu damu a kokarinmu na gina cigaba mai ɗorewa a Sokoto."
"A yau ina tabbatar maka da cewa APC da kafatanin mambobinta zasu yi aiki da kai da sauran 'yan tawagarka domin cika burin nasararmu a zabe mai zuwa."

- Aliyu Wamakko.

Legit.ng Hausa ta samu zantawa da wani jigon APC a jihar Sokoto, Mubarak Abubakar, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, yace jira kawai suke a sanar sun ci zaɓe a 2023.

Mista Abubakar ya shaida wa wakilin mu cewa jagoran APC, Aliyu Wamakko, ya kawo karshen mulkin PDP a Sokoto.

"Eh tabbas ɗan takarar gwamna da mafi yawan yan takarar PRP sun dawo APC. Mun ƙara karfi duk da ni a wuri na zan iya cewa babu wata jam'iyya a Sokoto banda APC."

Kara karanta wannan

Da Gaske Jam'iyyar PRP Ta Rushe Cikin APC a Sakkwato? An Fayyace Gaskiyar Lamari

"Dama can jam'iyyu biyu ne amma idan ka duba yadda mambobin PDP harda hadiman gwamna ke aje aiki suna shigowa APC kai kasan cewa mun kama hanyar nasara," inji shi.

Ya ƙara da cewa jm'iyar APC zata karbi Mulki daga jam'iyar PDP a jahar Sokoto da yardar Allah kuma wannan shine Ra'ayin Sakkwatawa.

A wani labarin kuma Atiku Abubakar da jam'iyyar PDP sun yi gagarumin rashin ƙungiyoyin magoya baya 10 a arewa ta yamma

Kungiyoyin, waɗanda ke tare da Atiku tun shekarar 2015 sun sauya sheka zuwa APC, sun cacci tsohon mataimakin shugaban ƙasa kan watsi da aikinsu.

Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya umarci a sanya mutanen cikin kwamitin yakin neman zaɓen Tinubu/Shettima na shiyyar don su ba da gudummuwarsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel