Ana Zargin Gwamna da Karbar Dala Miliyan 28 Domin Bata ‘Dan Takarar Shugaban Kasa

Ana Zargin Gwamna da Karbar Dala Miliyan 28 Domin Bata ‘Dan Takarar Shugaban Kasa

  • Gwamnan Anambra ya nesanta kan shi daga zargin da wasu magoya bayan Peter Obi suke yi masa
  • Farfesa Charles Soludo yace bai karbi kudin kowa da nufin ya kashewa tauraruwar Obi kasuwa ba
  • Soludo yace zai zauna da ‘Dan takaran na LP domin su dinke barakar da ke tsakaninsu kafin 2023

Anambra - Gwamnan jihar Anambra, Farfesa Charles Soludo ya yi fatali da zargin da ake yi masa na karbar kudi da nufin ya batawa Peter Obi suna.

Vanguard ta rahoto Charles Soludo yana mai cewa bai karbi Dala miliyan 28 da wasu ke rayawa da nufin ya kashewa Mr. Peter Obi kasuwa a zabe ba.

Soludo ya bayyana wannan ne a lokacin taya Rabaren Paulinus C. Ezeokafor murnar cika shekara 70 a wani cocin St. Patrick a garin Awka a Anambra.

Kara karanta wannan

Bayan Sauyin Launi, Buhari Ya Nuna Inda Sababbin Kudin da Aka Yi Suka Bambanta

Mai girma Gwamnan yace da yana karbar wadannan kudi, da yanzu ya shiga sahun Attajiran Najeriya. Independent ta tabbatar da wannan rahoto.

Obi ya ci karo da Soludo

Gwamnan na Anambra ya yi bayanin yadda ya zauna da Peter Obi mai neman zama shugaban Najeriya a karkashin jam’iyyar LP a daren da ya gabata.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Charles Soludo
Peter Obi da Farfesa Charles Soludo Hoto: independent.ng
Asali: UGC

"Idan da gaske na karbi $28m domin bata sunan ‘danuwana, Peter Obi, da nayi matukar kudi a halin yanzu.
Ga masu maganar bata suna da sauransu, har da masu cewa na karbi rashawa domin fadan abin da fada.
Na fada masu su kawo hujjojinsu, zan kuwa yi amfani da su a wajen ginawa mutanen jihar Anambra tituna.
Da a ce Soludo ya shiga harkar karbar rashawa, da yanzu na zama hamshakin wanda ya mallaki Tiriliyoyi."

Kara karanta wannan

Kwankwaso: Inda aka Samu Cikas, Maganar Taron Dangi da Peter Obi Ta Wargaje

- Charles Soludo

Farfesa Soludo ya yi maganar banbancinsa da Obi da wasu suke ganin hakan ya jawo aka ji Gwamnan yana neman bata lissafin ‘dan takaran na 2023.

“Babu sabani a tsakanin mutum da mutum tsakani na da Peter Obi. Babu wanda ya karbe matar wani. Sabaninmu a kan asalin manufar siyasa ne.
Game da sabanin da muke da shi, za mu hadu nan da ‘yan kwanaki. Mun amince za mu zauna, mu tattauna, mu shawo kan bambancinmu.”

- Charles Soludo

Son kai a NUPRC da NEITI

Labari ya zo cewa za a binciki abin da ke faruwa a hukumomin NUPRC da NEITI a Majalisar Wakilan Tarayya a sakamakon korafin da jama’a suke yi.

‘Dan majalisar APC, Hon. Hafizu Ibrahim Kawu yace hukumomin sun dauki ma’aikata ba tare da sun yi adalci a rabo ba, don haka sai an yi gyara.

Kara karanta wannan

Gwamna Ya Tsinci Kansa A Matsala Kan Sukar Peter Obi, Matasan Ibo Sun Bayyana Matakin Da Za Su Ɗauka A Kansa

Asali: Legit.ng

Online view pixel