Zaɓen Shugaban Ƙasa: Jihohin PDP 7 Masu Ƙarfi Da Atiku Zai Iya Shan Kaye A 2023

Zaɓen Shugaban Ƙasa: Jihohin PDP 7 Masu Ƙarfi Da Atiku Zai Iya Shan Kaye A 2023

  • Jam'iyyar hamayya na kokarin kawo karshen mulkin jam'iyyar APC a zaben 2023
  • Amma, rikicin cikin gida da wasu abubuwan na barazana ga nasarar dan takarar shugaban kasar jam'iyyar, Atiku Abubakar
  • A wannan rahoton, Legit.ng ta yi nazarin wasu abubuwa da ka iya saka Atiku shan kaye a wasu jihohin da PDP

A zaben shugaban kasa na Najeriya, galibi ana sa ran jam'iyyun siyasa su ci jihohin da gwamnoninsu ke mulki.

Hakan na yiwuwa ne saboda gwamnonin na da karfin fada a ji a jihohinsu kuma ana fatan za su yi wa dan takarar shugaban kasarsu aiki ya samu nasara.

Atiku
Zaben Shugaban Kasa: Jihohin PDP 7 Masu Karfi Da Atiku Zai Iya Shan Kaye A 2023. Hoto: Atiku Abubakar.
Asali: Facebook

Amma, a kan samu wasu lokuta da yan takarar shugaban kasa ke shan kaye a jihohin da gwamnonin da ke mulki yan jiharsu ne.

Wasu misalan jihohin da hakan ya faru shine jam'iyyar All Progressives Congress, APC, ce ke mulki a jihar Oyo kafin zaben 2019, inda marigayi Abiola Ajimobi ke mulki a matsayin gwamna.

Kara karanta wannan

"Mazi Tinubu": Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Na Jam'iyyar APC Ya Samu Sarauata A Yankin Su Peter Obi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Duk da haka, Shugaba Muhammadu Buhari ya sha kaye a jihar ga Atiku Abubakar na jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP.

Hakazalika, Buhari ya sha kaye hannun Atiku a jihar Imo, inda Rochas Okorocha ke mulki kafin zaben 2019.

Daya daga cikin dalilan da yasa Buhari ya sha kaye a jihohin na APC da aka ambata a lokacin shine rikicin cikin gida.

Hakan na iya faruwa da Atiku, wanda ya sake samun tikitin takarar zaben shugaban kasa na 2023 a 2023.

Gabanin babban zaben 2023, jam'iyyar ta APC mai mulki a halin yanzu na rike da jihohi 21 yayin da jam'iyyar hamayyar na da jihohi 14, ciki har da Osun, wacce ta samu a baya-bayan nan.

Jam'iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA) ne ke kula da sauran jihar wato Anambra.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Jerin wasu jihohi 5 na APC da Tinubu zai iya rasa kuri'unsu badi

Jihohin PDP 6 da akwai yiwuwar Atiku Abubakar ya sha kaye

Amma, cikin jihohin 14 da jam'iyyar PDP ke mulki, jam'iyyar na fama da rikicin cikin gida a jihohi shida, sune;

1. Ribas

2. Oyo

3. Abia

4. Enugu

5. Benue

6. Bauchi

Hudu cikin jihohin na yankin kudu, yayin da sauran biyu na arewacin Najeriya.

Jihar Filato ta yi alkawarin bawa Atiku kuri'u miliyan 2 a zaben 2023

A wani rahoton, jam'iyyar PDP a jihar Filato ya yi wa Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasarta alkawarin kuri'u miliyan biyu a zaben 2023.

Manyan yan jam'iyyar na PDP a jihar sun furta hakan ne yayin kaddamar da kwamitin kamfen din Atiku-Mutfwang a Jos, babban birnin jihar kamar yadda AIT ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel