Wakila Buhari Ya Jefa ’Yan Najeriya Cikin Yunwa, Amma Ya Dora Kasar Nan a Kan Turbar Ci Gaba, Inji Tinubu

Wakila Buhari Ya Jefa ’Yan Najeriya Cikin Yunwa, Amma Ya Dora Kasar Nan a Kan Turbar Ci Gaba, Inji Tinubu

  • Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC, Bola Tinubu ya bayyana yabonsa ga yadda Buhari ya ceto kasar nan daga rikita-rikita
  • Tinubu ya kuma bayyana cewa, akwai alamun Buhari ya tsoma 'yan Najeriya a yunwa, amma ya daura Najeriya kan turbar ci gaba
  • A lokuta da dama Tinubu ya sha yin alwashin ci gaba daga inda Buhari ya tsaya idan aka zabe a 2023

Arewa maso Gabas - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ya ce akwai yiwuwar 'yan Najeriya sun shiga matsanancin yunwa a mulkin Manjo Buhari mai ritaya, amma tabbas ya daura kasar nan a turbar ci gaba.

Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin kaddamar da mahakar man fetur da aka gina a Kolmani da ke tsakanin Gombe da Bauchi, TheCable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gara in Mutu da dai in Gazawa Magoya Bayana, Peter Obi

Tsohon gwamnan na jihar Legas ya ce, tarihi zai tuna da Buhari saboda shine tsohon janar din da ya zo ya cece Najeriya yayin da lamurra suka yi muni.

Tinubu ya ce akwai yunwa a mulkin Buhari, amma ya yi gyara
Wakila Buhari Ya Jefa ’Yan Najeriya Cikin Yunwa, Amma Ya Dora Kasar Nan a Kan Turbar Ci Gaba, Inji Tinubu | Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Tarihi zai yiwa Buhari adalci, inji Tinubu

A kalaman Tinubu:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Duk abin da suka fada a shafukansu na sada zumunta, martani na gargajiya dakuma rubuce-rubuce, tarihi zai yi adalci saboda kana cikin jerin janar din da suka yi ritaya suka dawo don ceto kasar.
"Watakila mun shiga halin yunwa, amma za mu jure; bamu son kashe junanmu. A yau, ka bamu hanyar ci gaba, hanyar nasara."

Tinubu ya kuma bayyana cewa, zai yi amfani da damar da Buhari ya gina don ci gaba da habaka tattalin arzikin kasar nan kamar yadda aka fara, Pulse ta tattaro.

Ba wannan ne karon farko da Tinubu ke yabawa gwamnatin Buhari ba, ya sha cewa zai daura mulkinsa ne daga inda Buharin ya tsaya idan aka zabe shi a 2023.

Kara karanta wannan

Yadda Gwmanan Jihar Ebonyi Ya Nuna Gyan Bayan Karara Ga Dan Takarar Jami'iyyar APC

Tinubu ya tsufa: Martanin APC game da batun da ake yadawa na kalaman El-Rufai

A wan labarin kuma, jam'iyyar APC ta yi karin haske kan batun da ake yadawa na cewa, gwamnan jihar Kaduna ya ce Tinubu ya tsufa wa mulkin Najeriya.

APC ta ce ana yada bidiyo ne kawai da ke son raba kan 'yan jam'iyyar, don haka El-Rufai bai fadi magana mai kama da wannan ba.

'Yan Najeriya na ci gaba da nuna damuwa game da lafiya da shekarun Tinubu, lamarin da ke kara dasa alamar tambaya kan dan takarar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel