Gwmnati Tana Sa Ido da Kyau, EFCC Tana Bibiyar Kudin da ‘Yan Takara Suke Kashewa

Gwmnati Tana Sa Ido da Kyau, EFCC Tana Bibiyar Kudin da ‘Yan Takara Suke Kashewa

  • Hukumar NFIU ta fitar da rahoton ayyukan da ta gudanar a shekarar bara da farkon shekarar nan
  • Daga cikin kokarin da tayi, NFIU tace ta ankarar da Jami’an tsaro a kan N150tr da aka yi yawo da su
  • Haka zalika, EFCC ta fara sa ido a kan ‘yan takaran 2023 saboda ganin ana shirin yin zabe a Najeriya

Abuja - Hukumar NFIU tayi wa mu'amalar kudi na fiye da Naira Tiriliyan 150 lamba tsakanin Junairu zuwa watan Maris na shekarar nan ta 2022 mai-ci.

Punch tace an yi wa wadannan ciniki alama ne a dalilin ana zargin akwai tambaya a kansu.

Wannan bayani yana cikin rahoton da hukumar ta fitar a ranar Lahadi. Hakan duk yana cikin kokarin da ake yi na sa wa ‘yan siyasa ido a gabanin zabe.

Kara karanta wannan

NDLEA Ta Cafke Mata Mai Shekaru 56 Dauke da Hodar Iblis Kan Hanyar Zuwa Saudiyya

Wasu majiya daga EFCC da NFIU sun shaidawa jaridar jami’an hukumomin suna aikin hadin-gwiwa tare domin su lura da kudin da suke yawo a yanzu.

Ana sabawa dokokin kasa

An zo lokacin da jam’iyyun siyasa, ‘yan takara da jiga-jigan jam’iyyu suke facaka da biliyoyi, har su sabawa dokokin yaki da safarar kudi da na ta’addanci.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

The Cable ta shaida cewa jami’an EFCC sun baza jami’ansu domin su rika bibiyar abin da ke shiga yana fita daga asusun masu neman takara a zaben 2023.

EFCC.
Shugaban EFCC Hoto: www.thecable.ng
Asali: UGC

Bankuna sun ankarar da hukumar NFIU a game da cinikin N150tr a kamfanonin inshora, kananan bankuna, kamfanoni da makamantansu suka yi a bana.

Kudi suna yawo ta bankuna

Rahoton yace adadin kudin da ke yawo da ake yi wa alamar tambaya ya karu da 23% a shekarar nan, idan har aka kamanta da abin da aka samu a shekarar bara.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Wike, Wasu Gwamnoni da Jiga-Jigan PDP Sun Sa Labule a Legas

A cikin mu'amala 2,845,927 da aka yi a farkon 2022, NFIU tace bankuna sun dauki nauyin 2,810,213.

A dokar kasa, hukumar ce take sa ido idan aka ga wasu kudi masu yawa suna yawo da ba a gane kansu ba, idan ana zargin an saba doka, sai a dauki mataki.

Barnar da ake tafkawa

A irin haka ne a shekarar da ta wuce, NFIU tace ta sanar da jami’an tsaro game laifffukan satar kudi 92, kauracewa biyan haraji 52, da na cin rashawa 52.

Sauran laifuffuka da aka gano sun hada da safarar kudi 101, harkar canji ba tare da bin doka 16, barazana 10, da taimakawa ta’addanci 9 da makamantansu.

13% na arzikin fetur

An samu rahoto ana zargin Gwamnoni masu arzikin fetur sun karbi biliyoyi daga bashin da suke bin Gwamnatin tarayya, amma suka yi gum da bakinsu

Sai da Gwamnan Ribas, Nyesom Wike ya fito ya yi bayani sannan mafi yawancin jama’a suka san jihohi sun zauna a kan Biliyoyin kudin da aka biya su.

Kara karanta wannan

An Kama ‘Yan Sa Kai dake Kai wa Boko Haram Bayanan Sirri da Kayayyakin Bukata

Asali: Legit.ng

Online view pixel