‘Dan Gwamna Yayi Kira ga Hukumomin Qatar da Su Halaka Duk Wanda ya Shiga Filin Wasa da Giya

‘Dan Gwamna Yayi Kira ga Hukumomin Qatar da Su Halaka Duk Wanda ya Shiga Filin Wasa da Giya

  • Bashir El-Rufai, ‘Dan gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya shiga kanun labarai sakamakon wata wallafa da yayi wacce ta janyo cece-kuce
  • A wallafar da yayi a Twitter, ‘dan Gwamnan ya bukaci hukumomi a Qatar da su kama, gurfanar tare da halaka duk wanda aka kama kama da giya a kasar
  • Wannan wallafar tashi kuwa ta janyo maganganu kala-kala yayin da wasu suke caccakarsa bayan fara gasar kwallon kofin duniya a kasar Musuluncin

Bayan dokoki masu tsauri da aka saka kan giya a gasar kwallon kafa ta kofin duniya a Qatar, Bashir El-Rufai, ‘dan Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna, ya bayyana matsayarsa kan lamarin.

Bashir El-Rufai
‘Dan Gwamna Yayi Kira ga Hukumomin Qatar da Su Halaka Duk Wanda ya Shiga Filin Wasa da Giya. Hoto daga The Governor of Kaduna
Asali: Facebook

A ranar Litinin, 21 ga watan Nuwamban 2022, Bashir ya je shafinsa na Twitter inda ya bayyana goyon bayansa kan haramta shan giya da hukumomin Qatar suka yi yayin gasar.

Kara karanta wannan

Za ta share talauci ne? Frashin tsintsiya 1 a N11,200 ya sa jama'a sun girgiza a intanet

Kamar yadda wallafarsa da Legit.ng ta gani a Twitter tace:

“Ina fatan a kama, gurfanarwa tare da halaka duk wanda aka samu ya shigar da giya filin wasan kasar da take da dokokin hani kan hakan.”

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Jama’a sun yi martani

Jim kadan bayan wannan wallafar, jama’a sun fusata da ita inda wasu suke kallonsa da maras son zaman lafiya tare da munafunci.

@realchado yace:

“Mutum zai goyi bayan Qatar kan kiyaye al’adarta amma kuma Bashir ‘dan El-Rufai yayi fatan halaka bakin haure kan giya. Ko da a ce ‘yan kasa ne, babu wani ladabtarwa ne baya ga wannan tsohon yayin? Dole ne kowanne laifi ya zama hukuncinsa kisa ne?

@KunleBoye yace:

“Cire kai? Ana kiranka da barawo amma kana rawa da akuya a hannu?”

@nmatopclass:

“Kisan tsoka ba shi ne bane kisa. Ana cewa, idan kaje gari ka gansu da bindi, kaima nema ganye ka saka. A mutunta al’adar jama’a.”

Kara karanta wannan

Duk Wanda Yace 2023 Lokacinsa ne, Ya Tafka Babban Kuskure, Kwankwaso Yayi Gugar Zana

@emmaneul_yours:

“Halaka mutum saboda ya shigar da giya filin wasa? Mun gode Allah kan cewa mutanen da aka fara aikowa da addinin Musulunci ba kauyawa bane kamar ka wanda kawai ke kwafar wani sashe na addinin.
“Babu shakka, hakan yasa kiyasin cigaban jama’a a arewacin Najeriya har yanzu yake kasa.”

Hotunan Bashir El-Rufai da matarsa sun tada kura

A wani labari na daban, hotunan kafin aure na Bashir El-Rufai da matarsa Halima Nwakaego kafin aure sun tada kura.

An ga ‘dan Gwamnan ya rike kugunta duk da ba a daura musu aure ba yayin da ita ma ta riko shi cike da so.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Online view pixel