2023: Matan Zamfara sun dau alkawarin kawowa Tinubu da Matawalle kuri’u masu yawan gaske

2023: Matan Zamfara sun dau alkawarin kawowa Tinubu da Matawalle kuri’u masu yawan gaske

  • Wata kungiyar mata ta APC a jihar Zamfara ta yi gangamin goyon bayan takarar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da Bello Matawalle
  • Kungiyar matan ta sha alwashin tabbatar da ganin mata sun fito kwansu da kwarkwatansu don zabar yan takarar jam'iyya mai mulki daga sama har kasa a zaben 2023 mai zuwa
  • Jagorar kungiyar, Dr Barira Ibrahim, ta ce ko shakka babu matan Zamafara APC zasu yi saboda irin moriyar da suke ci daga wajen uwargidar gwamna, Aisha Bello Matawalle

Zamfara - Kungiyar kwararrun mata na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) sun ayyana goyon bayansu ga takarar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da tazargen Gwamna Bello Matawalle da dukkanin yan takarar jam’iyya mai mulki a babban zaben 2023.

Shugabar kungiyar reshen jihar Zamfara, Dr Barira Ibrahim ce ta bayyana hakan a ranar Juma’a, 18 ga watan Nuwamba, yayin da take jawabi ga taron matan APC yayin wani gangami da ya gudana a Gusau, babban birnin jihar, PM News ta rahoto.

Kara karanta wannan

Kwanaki Kadan Bayan Kaddamar da Kamfe, Bola Tinubu Ya Yi Gagarumin Rashi a Jihar Arewa

Logon APC
2023: Kungiyar Mata a Zamfara Sun Ayyana Goyon Bayansu Ga Tinubu Da Matawalle Hoto: Nigerian Trinbune
Asali: UGC

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta rahoto cewa dubban mata sun halarci gangamin wanda ya fara daga cibiyar mata ta Gusau har zuwa gidan gwamnati.

Mata na taka rawar gani a siyasar Zamfara - Dr Barira

Kungiyar ta shirya taron mai taken: “Gyara da share Zamfara daga sama zuwa kasa”, domin ayyana goyon bayanta ga takarar Tinubu da Matawalle da kuma dukkanin yan takarar APC a jihar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Dr Barira ta bayyana cewa mata sun dade suna taka muhimmiyar rawar gani a jihar a lokacin zabe.

Ta ce:

"Saboda haka, dole mu ayyana goyon baya ga yan takarar da suka yiwa mata tanadi mai kyau.
"Dukkanin mata a Zamfara sun yarda cewa dole mu shiga siyasa don cimma mafarkanmu."

Ta yi alkawarin cewa mata zasu kawowa APC makamancin kuri'un da suka kawo a 1999, 2003, 2007, 2011, 2015 da 2019.

Kara karanta wannan

Aisha Buhari Ta Rangada Lalle na Musamman Mai Nuna 'Dan Takaranta a 2023

"Dama Zamfara gida ce ta APC, don haka, ba za a barwa jam'iyyun adawa kowace kujera ba.
"A matsayina na jagora a jiha, ina farin cikin sabar da cewa zamu tara sannan mu tabbatar da ganin ceea duk mata a garuruwanmu sun zabi daukacin yan takarar APC."

Mata masu ciki sun ci gajiyar shirin kiwon lafiya na uwargidar gwamna Matawalle

Ta yaba ma uwargidar gwamnan jihar Zamfara, Hajiya Aisha Bello Matawalle kan inganta rayuwar mata a jihar, rahoton Peoples gazette.

A cewarta, dubban mata a jihar sun amfana daga shirin tallafi na uwargidar gwamna Matawalle.

"Matanmu, musamman daga kasa, sun amfana da shirin kiwon lafiya wanda Hajiya Aisha Matawalle ta rabawa mata masu ciki kayayyakin kula da lafiya."

Dubban mambobin APC sun fice zuwa PDP a Sakkwato

Mun kawo a baya cewa jam'iyyar APC ta yi rasa dubban mambobinta a jihar Sakkwato inda suka sauya sheka zuwa babbar jam'iyyar adawar kasar ta PDP.

Kara karanta wannan

Dalilin Da Ya Sa Arewa Ke Goyon Bayan Tinubu, Sanata Mai Karfin Fada A Ji A APC Ya Magantu

Da yake tarban masu sauya shekar, dan takarar gwamna na PDP a Sakkwato, Mallam Umar ya dauki alkawarin tafiya da su a dukkanin harkokin jam'iyyar ba tare da nuna wariya ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel