Daga Karshe, Tsohon Gwamnan Dake Tsagin Wike Ya Faɗi Wanda Zai Goyi Baya a 2023

Daga Karshe, Tsohon Gwamnan Dake Tsagin Wike Ya Faɗi Wanda Zai Goyi Baya a 2023

  • Makusancin gwamna Wike kuma tsohon gwamnan Ekiti, Ayo Fayose, yace ba zai taba zagin Bola Tinubu ba
  • Fayose ya bayyana cewa duk da ba inuwarsu daya a siyasa ba amma Tinubu jagora ne na yarbawa
  • Da yake tsokaci kan matsayarsa a 2023, Fayose yace zai yi wa PDP aiki duk da rigimar dake wakana tsakani

Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose, yace zai goyi bayan ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, a babban zaɓen 2023 da ke tafe.

Mista Fayose ya bayyana wannan matsayar ne a wata hira da kafar watsa labarai Channels tv cikin shirin nan nasu mai suna Politics Today watau siyasa a yau.

Ayodele Fayose.
Daga Karshe, Tsohon Gwamnan Dake Tsagin Wike Ya Faɗi Wanda Zai Goyi Baya a 2023 Hoto: vanguardngr
Asali: UGC

Sai dai tsohon gwamnan yace zai nesanta kansa da zagin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, duk da sun raba jiha a siyasance.

Kara karanta wannan

'Na Maka Magiya Dan Allah' Ɗan Takarar Shugaban Kasa Ya Roki Wike Ya Goya Masa Baya a 2023

Jaridar Vanguard ta rahoto Fayose na cewa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Bari na faɗa muku idan mutane sun kasa kunne su ji na zagi Bola Tinubu don nuna musu bana tare da shi, to su sani ba zan yi haka ba."

Ya bayyana cewa duk da bambancin ra'ayin siyasa da gwamnonin arewa da jiga-jigan siyasa na yankin suke da shi da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ba zaka ji suna hantarar juna ba.

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa Ayo Fayose na ɗaya daga cikin makusantan gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, kuma ya nuna rashin jin daɗinsa da rigingimun PDP.

Fayose ya ayyana Bola Tinubu da jagoran yarbawa saboda haka ba zai ci mutuncin tsohon gwamnan jihar Legas ɗin ba duk da basu haɗa inuwa ɗaya ba a siyasa.

Jigon PDP yace yana ganin girman tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, kamar yadda yake girmama jagoran APC, Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Rigimar PDP: Tsagin Gwamna Wike G5 Sun Gindaya Sharudda a Sabon Shirin Sulhu da Su Atiku

Yace, "Idan har hanya ɗaya tilo da zan nuna ina adawa da Bola Tinubu a matsayina na Bayerabe shi ne na zage shi to ba zan taɓa yin haka ba."

"Ku saurare ni, Atiku da Tinubu sun haura shekara 70, me zaisa su tsaya suna zagi da hantarar Juna? Bana cikin masu zagin Tinubu, haka ba zan zagi Atiku ba."

Tsohon gwamnan yace zai yi wa PDP aiki duk da rigimar dake tsakanin Wike da Atiku tun bayan zaɓen fidda ɗan takarar shugaban ƙasa.

Adams Oshiomhole Ya goyi bayan Wike a rikicin PDP

A wani labarin kuma Tsohon shugaban APC na kasa, Kwamaret Adams Oshiomhole, yace Wike ne gwarzonsa na shekara

Oshiomhole, wanda ya kaddamar da katafiyar gadar da Wike ya gina, yace bai dace a rinka karya alƙawarin yarjejeniyar da aka ɗauka ba.

A cewarsa, jajircewar da Wike ya yi kan asalin matsayar gwamnoni kudu abun a yaba ne ba kuma wasu su koma suna yaƙarsa ba.

Kara karanta wannan

Gidana Ni Kadai Ne Musulmi, Dukkan Iyalina Kiristoci ne: Tinubu Ya Laburtawa CAN

Asali: Legit.ng

Online view pixel