Uwargidata Kirista Ce, Yarana Gaba Daya Kiristoci Ne, Ni Kadai Ne Musulmi a Gidana: Tinubu Ya Bayyanawa CAN

Uwargidata Kirista Ce, Yarana Gaba Daya Kiristoci Ne, Ni Kadai Ne Musulmi a Gidana: Tinubu Ya Bayyanawa CAN

  • Dan takara shugaban kasa, Bola Tinubu, ya yi zamansa da aka dade ana tsamanni da kungiyar CAN
  • Kungiyar CAN dai tuni tace ba zata goyi bayan Tinubu ba saboda ya zabi mataimaki Musulmi irinsa
  • Tinubu ya ce shi fa dalilin da ya sa ya dauki Shetima ba kowai bane illa zai fi jin dadin aiki da shi

Abuja - Dan takarar kujerar shugaban kasa karkashin jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Tinubu ya yi watsi da jita-jitan cewa yana kokarin Musuluntar da Najeriya.

Tinubu ya bayyana hakan ne ranar Laraba yayin ganawarsa da kungiyar Kiristocin Najeriya CAN, rahoton Vanguard.

Tinubu ya laburta musu cewa ko a gidansa Kiristoci sun fi yawa, shi kadai ne Musulmi, saboda haka idan ya gaza Musuluntar da iyalansa, ta yaya zai Musuluntar da Najeriya.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Tona Masu Lallaban Shi Wajen Samun Takarar Mataimakin Shugaban Kasa

A cewarsa:

"Jita-jitan da ake yadawa cewa ina shirin mayar da Kiristocin Najeriya saniyar ware ba gaskiya bane kuma da ban takaici. Bani da wata manufar yin hakan."
"Zaune da ni a nan uwargidata ce... Ban isa in yi takarar zabe a cikin gidana ba sbaoda zan sha kashi. Sukkansu na zuwa Coci ranar Lahadi su bar ni a gida."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tinubu da CAN
Uwargidata Kirista Ce, Yarana Gaba Daya Kiristoci Ne, Ni Kadia Ne Musulmi a Gidana: Tinubu Ya Bayyanawa CAN Hoto: @OfficialABAT
Asali: Twitter

Kiristoci 2 sukayi muki a Legas baya na

Tinubu ya kara da cewa da bai son Kiristoci, da bai basu mulki fiye da Musulmai a jiharsa ta Legas ba.

Tun bayan saukarsa daga mulki a 2007, Babatunde Fashola, ne kadai Musulmin da ya mulki Legas.

"Tun da na sauka daga mulkin Legas, an yi gwamna Musulmi daya, Kiristoci biyu."
"Dukkanku kun san Matata Kirista ce kuma Fasto. 'Yayana gaba daya Kiristoci ne. Ba zai yiwu in ci mutuncinsu ba, ba tare da na ci mutunci kaina ba. A matsayina na Uba mai mata Kirista da Yara Kiristoci, ire-iren wadannan zarge-zarge na bakanta min rai."

Kara karanta wannan

Zaɓen Shugaban Ƙasa Na 2023: Jerin Buƙatun Da Shugabannin CAN Suka Gabatarwa Tinubu A Abuja

Jam'iyyar APC ta kaddamar da Kamfe

A ranar Talata, Jam'iyyar APC ta kaddamar da yakin neman zabenta na shugaban kasa a garin Jos, babbar birnin jihar Plateau.

A kalla gwamnonin jam'iyyar APC ashirin da biyu (22) ne suka halarci taron tare da dimbin yan majalisar tarayya da na jiha

Asali: Legit.ng

Online view pixel