Kano: APC Ka Iya Shan Kaye a Zaben 2023, Doguwa Ya Magantu Bayan Barkewar Sabon Rikici

Kano: APC Ka Iya Shan Kaye a Zaben 2023, Doguwa Ya Magantu Bayan Barkewar Sabon Rikici

  • Hon. Alhassan Ado Doguwa ya yi gagarumin gargadi ga jam'iyyarsa ta APC a jihar Kano gabannin babban zaben 2023
  • Dan majalisar ya bayyana cewa idan har Ganduje bai farka ya karbe ragamar kula da harkokin jam'iyyar ba toh suna iya shan kaye a zaben
  • Wannan jan kunne na doguwa na zuwa ne bayan barkewar sabon rikici a jam'iyyar wanda ya kai ga sun yi musayar zafafan kalamai da dan takarar mataimakin gwamna, Murtala Garo

Kano - Shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai, Alhassan Ado Doguwa, ya yi gargadin cewa idan har manyan APC basu dauki cikakkiyar iko kan jam’iyyar ba a jihar Kano, toh za su iya shank aye a zaben 2023, jaridar Guardian ta rahoto.

Doguwa na so Gwamna Abdullahi Ganduje ya karbi ragamar kula da harkokin jam’iyyar mai mulki don duba yadda tsohon kwamishinan harkokin kananan hukumomi kuma dan takarar mataimakin gwamnan APC, Murtala Garo ke wuce gona da iri.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Atiku ya samu nakasu a Sokoto, manyan jiga-jigai sun koma APC

Alhassan Doguwa
Kano: APC Ka Iya Shan Kaye a Zaben 2023, Doguwa Ya Magantu Bayan Barkewar Sabon Rikici Hoto: @alhassan.doguwa
Asali: Facebook

Da yake jawabi ga manema labarai a Kano kan sabon rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar, Doguwa ya koka cewa idan har ba a magance batun ficewar mamabobin majalisar dokokin kasa bakwai ba a Kano, APC na iya rasa mulki a jihar.

Dan majalisar ya yi kira ga gwamnan kan ya ceto jam’iyyar daga durkushewa da ayyukan wasu yan tsirarun mutane da ke kewaye da shi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jaridar Vanguard ta nakalto Doguwa yana cewa:

“Hatsarin da muke ciki shine muna da wasu mutane kewaye da shi (Ganduje), idan ba a dauki mataki ba, idan Ganduje bai karbe ragamar kula da harkokin jam’iyyar ba, toh labarin APC a zabe mai zuwa zai zama mara dadi. Muna fuskantar adawa da ba a taba samun irinsa ba. Adawar APC a nan Kano na da tsanani kuma yana iya zama mai hatsari.

Kara karanta wannan

Ta karewa APC a jihar a wata Arewa, dan takarar sanata da masoyansa sun koma ADC

“Don haka ina amfani da wannan damar don yin kira ga Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da ya gaggauta fitowa sannan ya karbe harkokin jam’iyyar da kuma gudanar da shirin kamfen dinmu kai tsaye. Saboda idan ya bar harkokin jam’iyyar a hannun mutanen da basu da kankan da kai, a zasu kashe jam’iyyar.”

Kafin wannan gargadi da Doguwa yayi, an tattaro cewa dan majalisar sun samu sabani da Garo lamarin da ya kai ga ba hammata iska.

An tattaro cewa lamarin ya faru ne a yammacin ranar Litinin lokacin da Doguwa ya shiga wani taron masu ruwa da tsaki na APC da ya gudana a gidan mataimakin gwamnan jihar da ke Bompai.

Doguwa wanda ya je taron ba tare da an gayyace shi ba ya yi korafi kan mayar dasu saniyar ware da shi da yan majalisar dokoki.

Sai dai Doguwa yace bai je wajen taron jam’iyyar domin fada da Garo ba, ya je ganin shugaban jam’iyya ne.

Kara karanta wannan

2023: Mutane Sun Fito Yayin da Ɗan Takarar AAC Ya Buɗe Kamfen Neman Gaje Buhari a Kano

2023: Gaskiyar Abun da Ke Tsakanina Da Wike, Ortom da Sauran Jiga-Jigan PDP, Peter Obi Ya Fasa Kwai

A wani labarin, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party (LP), Peter Obi ya yi bayani kan gaskiyar alakar da ke tsakaninsa da wasu fusatattun gwamnonin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Obi ya ce yarjeniniya guda da ke tsakaninsa da gwamnonin na PDP ya kasance a kan ra'ayinsu na son mayar da Najeriya kasa mai inganci.

Ya yi bayanin ne a ranar Talata, 1 ga watan Nuwamba, yayin da yake jawabi a Makurdi a wata ziyara da ya kaiwa gwanan jihar Benue, Samuel Ortom, jaridar Vanguard ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel