Ba Zamu Yarda Wani Dan Arewa Ya Gaji Buhari Ba: Kungiyoyin Kasar Yarbawa

Ba Zamu Yarda Wani Dan Arewa Ya Gaji Buhari Ba: Kungiyoyin Kasar Yarbawa

  • Yakin neman zaben wanda zai zama shugaban kasa bayan shugaba Buhari ya fara daukan zafi
  • Wasu kungiyoyin yakin neman zaben Tinubu sun ce wajibi ne mulki ya bar Arewa a shekarar 2023
  • Cikin manyan yan takara hudu da ake ganin daya zai lashe zaben na 2023, biyu yan yankin Arewa ne

Kungiyoyin yakin neman zaben jam'iyyar All Progressives Congress APC a jihar Ondo sun lashi takobin cewa zasu yi iyakan kokarin don ganin wani dan Arewa bai gaji Shugaba Buhari ba.

Kungiyoyin sun goyon bayan tsohon gwamnan Legas, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Sun hada da Tinubu Independent Action Movement (TIAM), Rontex for BAT da Asiwaju Progressives Diaspora (APG).

Alasdrua
Ba Zamu Yarda Wani Dan Arewa Ya Gaji Buhari Ba: Kungiyoyin Kasar Yarbawa
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Gida Bai Koshi Ba: Kungiyar Yarbawa Ta Bayyana Wanda Take So Ya Gaje Buhari Tsakanin Obi Da Tinubu

Shugaban TIAM kuma tsohon karamin Ministan Neja Delta, Sanata Tayo Alasoadura, ya bayyana cewa su dai suna da dan takara gwanin tallatawa.

Ya bayyana hakan ne a bikin kaddamar da kungiyar a Akura, birnin jihar Ondo, rahoton TheNation.

Sanata Alaosadura ya ce mambobin TIAM za suyi aiki tukuru ba tare da taimakon wani ba don ba da nasu gudunmuwan wajen ganin Tinubu ya lashe zaben a jihar Ondo.

Yace:

"Muna da abin tallatawa. Asiwaju Bola Ahmad Tinubu shi ne mai nasara a koda yaushe."

A bangarenta, shugabar kungiyar Rontex for BAT, Mrs Saratu Funke Adelakun, tace an hada mata sama da 5000 da zsu shiga lungu da sako don tallata Tinubu.

Adelakun tace wajibi ne mulki ya dawo yankin kudu maso yamma a 2023 kuma ta yi kira da shugabannin kungiyoyin su tabbatar jama'ar yankunansu sun mallaki katin zabe.

Kungiyar Yarbawa Ta Bayyana Wanda Take So Ya Gaje Buhari Tsakanin Obi Da Tinubu

Kara karanta wannan

Tinubu: Abin da Buhari Ya Fada Mani Yayin da Na Nemi Ya Zakulo Mani Mataimakina

A wani labarin kuwa, Shugaban kungiyar kare muradun yan kabilar Yarbawa ta Afenifere, Pa Reuben Fasoranti, ya jadadda cewa shi dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya lamunce mawa.

Pa Fasoranti, wanda ya ce har gobe shine shugaban Afenifere, ya ce kungiyar bata tsayar da dan takarar jam’iyyar Labour Party, Mista Obi ba

A wani bidiyo da ya yadu, an gano dattijon mai shekaru 97 yana nuna cewa yana sane da abubuwan da suka faru a kungiyar ta Afenifere.

Asali: Legit.ng

Online view pixel