PDP Za ta Ci Duka Zaben da Za Ayi, Ban da na Kujerar Shugaban kasa Inji Gwamnanta

PDP Za ta Ci Duka Zaben da Za Ayi, Ban da na Kujerar Shugaban kasa Inji Gwamnanta

  • Gwamna Nyesom Wike ya rantsar da Hadiman da ya zaba domin suyi masa aiki a mazabun jihar Ribas
  • A wajen bikin rantsarwar, Gwamnan ya yi hasahen PDP za ta lashe kujerun 2023, ban da shugaban kasa
  • Wike ya dauki lokaci ya caccaki Dr. Abiye Sekibo, wanda yana cikin mutanen Atiku Abubakar a Ribas

Port Harcourt – Gwamna Nyesom Wike ya fara cika-bakin cewa jam’iyyar PDP za ta lashe duk wani zabe da za ayi a 2023 a jihar Ribas da yake mulki.

Mai girma Nyesom Wike yace zaben da PDP ba za tayi nasara ba shi ne na kujerar shugaban kasa, Wike ba ya ganin nasarar Atiku Abubakar a haka.

Vanguard ta rahoto Wike yace muddin ba ayi abin da ya dace ba, PDP za ta sha kashi a babban zabe.

Kara karanta wannan

Ganduje Ba Zai Ruguza Mani Gida ba, ko da a kan Layin Lantarki aka Gina Inji Rarara

Gwamnan ya yi wannan bayani ne a ranar Litinin 31 ga watan Oktoba 2022 yayin rantsar da sababbin Hadimai 319 da ya nada da za suyi masa aiki.

Za mu ci duk wasu kujeru - Wike

Kamar yadda tsohon Ministan tarayyar ya fada, PDP za ta lashe kujerun majalisar dokoki na jihohi da na majalisun tarayya da na Sanatoci, da Gwamna.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Idan aka zo kan zaben shugaban kasa kuwa, Nyesom Wike yace har yanzu ba su dauki matsaya ba, yace dole sai jam’iyyar ta su tayi abin da ya kamata.

Gwamnonin PDP
Wike da wasu Gwamnonin PDP Hoto: @Topboychriss
Asali: Twitter

Har ya gama jawabi, Gwamnan bai yi bayanin abin da yake nufi da shi ne abin da ya kamata ba. An san tun zaben fitar da gwani aka samu sabani da shi.

“Jam’iyyar PDP za tayi nasara a jihar mu. Ba na boye wannan idan maganar takarar ‘yan majalisar dokoki da tarayya da na Sanatoci ake yi.

Kara karanta wannan

2023: Rikicin PDP Ya Kara Dagulewa, Shugaban Jam'iyyar Ya Yi Fatali da Shawarin Dattawa

Dayan da ya rage (shugaban kasa), ba mu yanke shawara ba tukuna, har sai an yi abin da ya dace. - Gwamna Nyesom Wike.

Wike ya soki mutumin Atiku

A wajen wannan bikin rantsarwa, Gwamna Wike ya caccaki tsohon Ministan sufuri na tarayya, Dr. Abiye Sekibo wanda ya kira ‘dan siyasar da ya gaza.

An rahoto Gwamnan yace Sekibo ya yi Ministan sufuri a lokacin da Atiku Abubakar Abubakar yake mataimakin shugaban kasa, amma Ribas ba ta amfana ba.

Shi kuwa Wike yace a lokacin da ya yi Ministan ilmi, ya daga darajar makarantu irinsu Kenule Beeson Saro-Wiwa Polytechnic da jami’ar Ignatius Ajuru.

Afenifere za su bi Tinubu

Rahoto ya zo cewa jagororin Afenifere sun warware mubaya’ar da Shugabansu ya yi wa Peter Obi, sun ce Bola Ahmed Tinubu ne wanda za su zaba a 2023.

Dattawan Yarbawa daga jihohin Legas, Oyo, Ogun, Ondo, Osun, Ekiti da Kwara da Kogi za su goyi bayan APC a zaben shuagaban kasa, kamar yadda suka fada.

Kara karanta wannan

2023: Al'amura Sun Canja Yayin Da Tsohon Ministan Buhari Ya Bayyana Goyon Bayansa Ga Tinubu, Ya Bada Dalili

Asali: Legit.ng

Online view pixel