Jerin Duka Abubuwan da Kwankwaso Ya Yi Alkwarin Zai Yi Idan Aka Zabe Shi a NNPP

Jerin Duka Abubuwan da Kwankwaso Ya Yi Alkwarin Zai Yi Idan Aka Zabe Shi a NNPP

  • Mun tattaro alkawuran da Rabiu Musa Kwankwaso ya yi wa ‘Yan Najeriya a takardar manufofinsa
  • Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya gabatar da manufofin da yake da shi idan ya zama shugaban kasa
  • Manyan alkawura 20 ‘Dan takaran ya fito da su a takaice, mun jero su ta hanyar hade wasu a wuri daya

Legit.ng Hausa ta samu ganin wannan takarda manufofin ‘dan takaran shugaban kasar na NNPP, ta kawo muhimman alkawuran da ke ciki:

1. Jagoranci da Adalci

Shafi na biyu na takardar alkawuran ya nuna za a samu jagoranci mai dauke da kishin kasa, gaskiya, sanin ya kamata, ke-ke-da-ke-ke da kuma adalci idan Rabiu Kwankwaso ya karbi mulki.

2. Zaman lafiya da Hadin-kai

‘Dan takaran ya yi alkawarin tabbatar da zaman lafiya da tsare rayuka da dukiyoyi, yace zai magance matsalolin satar mutane, fasa bututun mai, rikicin manoma-makiyaya da dai sauransu.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum Ya Tuna da Iyayensu, Ya Dauko Marayu, Zai Kashe Masu N300m

3. Farfado da tattalin arziki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin Kwankwaso za ta fito da tsare-tsaren gyara ta hanyar ceto tattalin arzikin kasa, samar da ayyukan yi ga matasa, da kuma kawo dabaru masu daurewa da za su kawowa kasa cigaba.

4. Ilmi mai nagarta

Daga cikin alkawuran ‘dan takaran akwai farfado da ilmi, yace ba zai gina sababbin makarantu ba, amma za a maida hankali wajen inganta wadanda ake da su domin samun nagartaccen ilmi.

5. Kiwon lafiya

Idan Kwankwaso ya kafa gwamnati, ya sha alwashin gyara bangaren kiwon lafiya a Najeriya. ‘Dan siyasar yace za a kara yawan malaman lafiya, kuma a cirewa mata kudin ganin likita.

6. Lantarki

‘Dan siyasar ya fahimci sai da wannan ne za a habaka tattalin arziki, yace zai tabbatar an samu isasshen wutan lantarki mai araha da daurewa ta yadda za a kawowa Najeriya cigaba.

Kara karanta wannan

Rabiu Kwankwaso Ya Yi Alkawarin Maida WAEC, NECO, JAMB Kyauta Idan Ya Gaji Buhari

7. Magance talauci

Gwamnatin NNPP za tayi maganin talauci a Najeriya. Rabiu Musa Kwankwaso yace zai tabbata abinci, ilmi da tufafi da sauran abubuwan more rayuwa ba su karfin talaka a kasar nan ba.

8. Abubuwan more rayuwa

Wani alkawari da Rabiu Musa Kwankwaso ya dauka shi ne gwamnatinsa za ta kawowa kowane yanki cigaba, yace za ayi wa dukkan wani bangare adalci wajen samar da abubuwan more rayuwa.

9. Bin doka da tsarin mulki

Idan NNPP ta kafa gwamnati, ‘dan takaranta ya yi alkawari ba za a rika yi wa doka hawan kawara ba, yace dokar kasa za tayi aiki a kan kowa, kuma kowa zai sha romon damukaradiyya.

10. Hulda da kasashen ketare

Daga cikin manufofin Rabiu Kwankwaso shi ne ya gyara kallon da ake yi wa Najeriya a Duniya, kuma ya inganta alakarmu da sauran kasashe, ya sa Najeriya jagoranci a fadin nahiyar Afrika.

Kwankwaso
Rabiu Kwankwaso ya gabatar da manufofi Hoto: @KwankwasoRM
Asali: Twitter

11. Aikin gwamnati ‘Yan fansho

‘Dan siyasar ya yi alkawarin ba zai yi watsi da hakkokin dattawan da suka yi wa kasa wahala da kuruciyarsu ba, sannan yace zai gyara aikin gwamnati, ya dawo masa da kimar da ya yi a baya.

Kara karanta wannan

2023: Abinda Ya Kamata 'Yan Najeriya Su Tambayi Kowane Mai Burin Gaje Buhari, Dattawan Arewa

12. Harkar noma da abinci

Za a sa ran idan jam’iyyar NNPP ta karbi mulki a samu isasshen abinci ta hanyar zamantar da aikin gona. ‘Dan takaran ya tabo harkar noma da kiwon dababbobi domin bunkasa sha’anin gona.

13. Mallakar gida

Baya ga hakkin tsofaffin ma’aikata, ‘Dan takaran NNPP yace zai maida hankali wajen ganin mallakar gida ya yi sauki ta hanyar hada-kai da bankuna da kuma gina gidaje ga al’umma.

14. Miyagun kwayoyi

Wani bangare da takardar manufofin ‘dan takaran ta duba shi ne ‘yan shaye-shaye. Gwamnatin NNPP za ta magance wannan matsala wanda tushe ce wajen kawo rashin tsaro da tattalin arziki.

15. Muhalli

Manufofin ‘dan takaran sun duba matsalar sauyin yanayi da muhallin al’umma. Kwankwaso zai bada karfi domin takaita annoba irinsu ambaliya, kwararowar hamada da zaizayewar kasa.

16. Nishadi

Har bangaren nisahadi sai da ya samu kula a manufofin ‘dan takaran shugaban kasar. Za a kula da bangarem domin samar da aikin yi, kawo kudin shiga, wanzar da zaman lafiya da tsare al’adu.

Kara karanta wannan

Shettima Ya Magantu Kan Tattaunawa da Kwankwaso Ya Koma Bayan Tinubu a Zaben 2023

17. Tsarin cigaban kasa

Gwamnatin Rabiu Kwankwaso za ta dawo da tsarin cigaban kasa da aka sani a baya, wannan zai kasance tubali wajen duk wasu tsare-tsare da manufofi da gwamnatin tarayya za ta fito da su.

Za a ba ilmi muhimmanci

Kun ji labari Sanata Rabiu Kwankwaso mai takara a New Nigeria Peoples Party zai ba ‘ya ‘yan talaka damar zuwa makarantun gaba da sakandare a cikin sauki.

Kamar yadda ya yi yunkuri a Majalisa, Gwamnatin Kwankwaso za ta sa sakamakon JAMB ya iya yin shekaru hudu, kuma WAEC da NECO za su zama kyauta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel